Gwamnatin Ganduje ta hana yara zuwa Otal, Ninkaya a ruwa maza da mata da wasu sabbin dokoki a Kano

Gwamnatin Ganduje ta hana yara zuwa Otal, Ninkaya a ruwa maza da mata da wasu sabbin dokoki a Kano

  • Gwamnatin jihar Kano ta kafa wasu sabbin dokoki da suka shafi Otal, wuraren cin abinci da shakatawa da kuma ɗakunan taron biki
  • Gwamnatin karkashin gwamna Ganduje ta hana shan shisha, zuwan yara Otal, luwadi da madigo da sauran su
  • Tace daga yanzun wajibi kowane mai dakin taron shagalin biki ya rufe wurin sana'arsa da karfe 11:00 na dare

Kano - Jami'an kula da wuraren shakatawa na jihar Kano, sun hana ƙananan yara zuwa Otal a faɗin jihar Kano, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta rahoto.

Jami'an sun kuma haramta shan Shisha, ninkaya a kwatamin ruwa tsakanin maza da mata, luwadi da kuma madugo.

Kazalika kwamitin ya sake nazari kan dokokin da suka halasta kafa wuraren cin abinci. Otal-Otal da kuma ɗakin taro a Kano.

Kara karanta wannan

Atiku ya aike da muhimmin sako ga hukumomin tsaro kan kisan mutum 200 a Zamfara

Gwamnan Kano, Dakta Ganduje
Gwamnatin Ganduje ta hana yara zuwa Otal, Ninkaya a ruwa maza da mata da wasu sabbin dokoki a Kano Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shugaban kwamitin, Baffa Babba Ɗan-Agundi, shi ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan fitowa daga taro tare da masu Otal, wuraren cin abinci da ɗakunan taro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ɗan-Agundi, ya shaida musu cigaban da aka samu na dokokin da kuma sabuwar tara da gwamnatin jiha ta tanada wanda zai taimaka wajen tsaftace wurin sana'arsu domin kaucewa aikata ba dai-dai ba.

A jawabinsa yace:

"Wani sashin abubuwan da muka tattauna shi ne, dakatar da kananan yara da ba su kai shekara 18 ba zuwa Otal, hana shan Shisha, ninkaya tsakanin mace da namiji, maɗugo da kuma luwaɗi."

Zamu sa ido kan taron shagalin biki da masu kiɗa

Hakanan shugaban kwamitin yace zasu sake nazari kan masu aikin saka kida a wurin biki da kuma su kan su wuraren taron shagalin biki.

"Nan gaba kwamitin mu zai sa ido kan masu sa kiɗa a wuraren biki, da manyan dakunan taro. Karfe 11:00 a garkame duk wani ɗakin taro."

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Sabon rahoto ya fallasa yadda Hafsoshin soji suka wawure dala biliyan $15bn kudin makamai

Jim kaɗan bayan kammala taron a gidan gwamnati, Gwamna Ganduje ya kaddamar da sabbin motoci sama da 8 domin saukaka aikin kwamitin.

A wani labarin na daban kuma Wata amarya a jihar Kano tace ga garin ku nan wata ɗaya kacal da daura aurenta

Amaryar mai suna Fatima Balarabe Haruna, ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya, wata ɗaya da kwana biyar bayaj kaita ɗakin mijinta

Wannan lamari ya jefa iyalanta cikin bakin ciki da takaici, amma mahaifinsa yace sun gode wa Allah da ya ba su ita, kuma ya karbi kayansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel