Yadda Gobara ta kama kasuwar Nguru dake jihar Yobe ranar Asabar
- Jama'ar Nguru a jihar Yobe sun waye gari da labarin mumunar gobarar da taci kasuwarsu da dukiyoyinsu
- Akalla shaguna 300 suka kone kurmus cike da dukiyar miliyoyin naira
- Gwamnan jihar ya bukaci ayi lissafin irin asarar da akayi don sanin tallafin da gwamnati za tayi
Yobe - Shahrarriyar kasuwar karamar hukumar Nguru dake jihar Yobe ta kama da wuta da safiyar Asabar, 8 ga watan Junairu, 2022.
Wani mai idon shaida, Abubakar Ibn Usman, ya ce shaguna dauke da kayan miliyoyi sun kone kurmus.
Akalla shaguna 300 ne wannan mumunar gobarar ta shafa, riwayar TheCable.
Shugaban kungiyar yan kasuwan, Ibrahim Adam, ya bayyana cewa gobarar ta fara ci ne misalin karfe 7 na safe.
Adam yace wutan lantarkin da aka kawo mai karfi ne ya haddada gobarar.
Ya yi kira ga Gwamnatin jihar su taimaka wajen sake gina kasuwar saboda tana da muhimmanci ga al'ummar yankin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya siffanta gobarar matsayin abin takaici.
Gwamnan ya umurci hukumar bada agaji na gaggawa tayi lissafin asarar da akayi don sanin abinda zai yi.
Wata mota ta kama da wuta a kan gadar Mainland ta jihar Legas
A bangare guda, wata mota kirar bas dauke da buhunna ta kama wuta a karshen gadar Third Mainland a jihar Legas.
Bidiyon faruwar lamarin da Legit.ng ta gani ya nuna wani kaso mai yawa na motar bas din da tuni ya kama da wuta wanda hakan ya sa ababen hawan da ke zuwa su ci gaba da bin hanyoyin da ke nesa da wajen saboda tsananin hayaki da zafi da take tashi.
Asali: Legit.ng