Rashin biyan hakkoki: Ma’aikatan Majalisar Tarayya sun sa ranar da za su fara yajin-aiki
- Kungiyar Parliamentary Staff Association of Nigeria ta yanke shawarar tafiya yajin-aiki a Najeriya
- Daga ranar 10 ga watan Junairu, ‘yan kungiyar PASAN da ke aiki a Majalisa za su shiga yajin-aikin
- Ma’aikatan su na zargin an saba dokar National Minimum Wage Act, 2019, an hana su hakkokinsu
FCT, Abuja - Ma’aikatan da ke aiki a majalisar tarayya a karkashin lemar Parliamentary Staff Association of Nigeria sun yanke hukuncin tafiya yajin-aiki.
A wani rahoto da ya fito daga Punch a ranar Alhamis, 6 ga watan Junairu, 2022, an ji kungiyar Parliamentary Staff Association of Nigeria za ta shiga yajin-aiki.
Ma’aikatan majalisar sun cin ma wannan matsaya ne domin nuna rashin jin dadinsu a kan yadda aka gagara biyansu tulin albashi da alawus da sauran hakkoki.
A wani zama da aka yi a jiya a Abuja, ‘yan kungiyar PASAN na reshen majalisar tarayya da hukumar majalisa, sun hadu a kan cewa za su daina zuwa ofis.
Za a dawo a ga ma'aikata sun yi yajin-aiki
Jaridar tace ma’aikatan za su rufe wuraren aikin na su ne ana saura mako daya Sanatoci da ‘yan majalisar wakilan tarayya su dawo daga hutun karshen shekara.
Yayin da ake sa ran a dawo aiki a majalisar Najeriya a ranar 18 ga watan Junairun nan, su kuma ma’aikatan za su daina aiki ne daga ranar 10 ga watan Junairun.
‘Yan kungiyar Parliamentary Staff Association of Nigeria wanda aka fi sani da PASAN, sun zargi Akawun majalisa, Ojo Amos da rashin cika alkawarin da aka yi.
PASAN ta aika wasika
Sahara Repoters tace PASAN ta aikawa Akawun majalisa takarda a kan batun kudinsu da suka makale.
Shugaban PASAN na reshen majalisar tarayya, Sunday Sabiyi da mataimakinsa, M. A. Liman suka sa hannu a wannan takarda da aka raba ta ko ina a majalisa.
Sabiyi da M. A. Liman sun sanar da shugabannin majalisa, Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila da jami’an DSS game da shirin tafiya yajin-aikin a makon gobe.
Kukan da PASAN take yi
A cewar ma’aikatan, ba a fara biyansu da sabon tsarin albashi ba har Disamban 2021 ta wuce, sannan kuma su na bin wasu alawus har na tsawon watanni 15.
Baya ga haka, ma’aikatan sun ce su na bin bashin tallafin kudin hayar gida na watanni takwas tare da wasu hakkokin da ya kamata a biya wadanda suka yi ritaya.
Asali: Legit.ng