Ba za ku tsira ba: Buhari ya magantu kan masu koma wa APC don gujewa EFCC

Ba za ku tsira ba: Buhari ya magantu kan masu koma wa APC don gujewa EFCC

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake magantuwa kan manufarsa ta yakar cin hanci da rashawa a Najeriya
  • Shugaban ya ce, komawar wani jam'iyya mai ci ta APC ba zai hana a gurfanar da mutum a gaban kuliya ba
  • Ya fadi haka ne yayin zantawa da gidan talabijin na NTA, tattaunawar da aka yada a yau Alhamis 6 ga watan Janairu

Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu wanda ake zargi da cin hanci da rashawa da zai tsira saboda ya koma jam’iyyarsa ta APC, Premium Times ta tattaro.

Buhari ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na NTA a ranar Alhamis 6 ga watan Janairu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Ba za ku tsira ba: Buhari ya magantu kan masu koma wa APC don gujewa EFCC | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

‘Yan Najeriya da dama na ganin cewa ‘yan siyasa a tsagin adawa da ake zargi da cin hanci da rashawa ko kuma aka gurfanar da su a gaban kuliya bisa zargin cin hanci da rashawa suna kaura zuwa jam’iyyar APC ne don gudun kada a hukunta su.

Kara karanta wannan

Gazawa: Buhari ya bayyana abin da yake ji a ransa idan aka ambaci PDP a kusa dashi

Wasu ‘yan siyasa da ake zargi da cin hanci da rashawa da suka koma jam’iyya mai mulki sun hada da tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode da kuma ‘yar majalisar dattawa, Stella Oduah.

Buhari, ya ce shiga jam’iyyar APC ba ya wanke duk wanda ake zargi da cin hanci da rashawa daga a kasar.

Gazawa: Buhari ya bayyana abin da yake ji a ransa idan aka ambaci PDP a kusa dashi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gazawa ce ke zuwa a zuciyarsa a duk lokacin da aka ambaci jam’iyyar PDP.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a daren Laraba, 5 ga watan Janairu, wacce Legit.ng ta bibiya.

Da aka tambaye shi kan abin da ke zuwa a ransa a lokacin da aka ambaci jam’iyyar adawa, Shugaba Buhari ya amsa da cewa, “gazawa”.

Kara karanta wannan

Shahararren mawaƙin Najeriya, Wizkid, ya ce bai yarda da addini ba

Jam’iyyar PDP ta mulki Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2015 lokacin da jam’iyyar APCta karbi mulki bayan shugaba Buhari ya doke tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a babban zaben 2015.

A wata hirar, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bai bada takamaimen amsa ba a yayin da aka tambaye shi game da wanda yake so ya zama magajinsa.

Da aka yi hira da Mai grima Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 5 ga watan Disamba, 2021 an bijiro masa da maganar wanda yake so ya karbi mulki a 2023.

Legit.ng Hausa ta bibiya wannan hira inda shugaban kasar ya nuna bai da wani ‘dan takara da yake da shi a rai, wanda zai so ya mikawa ragamar mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.