Ina son yan Najeriya suce na yi iyakan kokari na, Shugaba Muhammadu Buhari

Ina son yan Najeriya suce na yi iyakan kokari na, Shugaba Muhammadu Buhari

  • Shugaba Buhari ya sake zantawa da yan jarida don amsa tambayoyin dake zukatan yan Najeriya
  • Shugaban kasan yace burinsa shine yan Najeriya suce ya yi iyakan kokarinsa
  • Bayan hirarsa da ChannelsTV da aka haska ranar Laraba, an kuma haska sabuwa da tashar NTA

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yiwa yan Najeriya iyakan kokarinsa kuma yana sa ran idan ya sauka daga mulki zasu fadi hakan da kansu.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne yayin hirarsa a gidan talabijin na NTA da aka haska ranar Alhamis.

Buhari yace:

"Abinda nike sa ran yan Najeriya suce shine mutumin nan ya yi iyakan kokarinsa."

Buhari ya bayyana cewa idan ya sauka daga mulki zai huta sosai saboda ya aikatu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Malam Ibrahim Shekarau Sha-Sha-Sha Ne, Allah Ya Tsine Masa: Fani-Kayode

Shugaba Muhammadu Buhari
Na yiwa yan Najeriya iyakan kokari na, Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: Aso Villa
Asali: Depositphotos

Don ka yi karatu bai zama dole ka samu aikin Gwamnati ba, Buhari ga Matasan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga matasan Najeriya suyi amfani da ilmin da suka samu a makaranta da wayewa wajen inganta kawunansu sabanin dogaro kan aikin gwamnati.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin hira ta musamman da gidan talabijin ChannlesTV ranar Laraba.

"Na so idan suka je makaranta; suka yi kokari; suka samu digiri, kada suyi tunanin dole ne sai gwamnati ta basu aiki," ya bayyana.

"Ka nemi ilimi ne saboda mai ilimi ya fi mara shi, ko wajen fahimtar matsalolin kai. Saboda haka ba a neman ilimi don gwamnati ta bada aiki ko kuma abinda turawan mulkin mallaka suka dasa mana a kai na cewa sai ka yi mota, ka yi gini, kana zuwa aiki karfe 8 ka dawo karfe 2."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng