Magidanci ya lakadawa budurwa dukan tsiya, ya umarci matarsa ta kashe ta a Kano

Magidanci ya lakadawa budurwa dukan tsiya, ya umarci matarsa ta kashe ta a Kano

  • Rundunar yan sanda reshen jihar Kano ta gurfanar da wani mutumi, Ahmadu Muhammad, a gaban kotu bisa zargin razana wata mace a jihar Kano
  • Mai gabatar da kara, Insufekta, Abdul Wada, yace wanda ake ƙara ya lakadawa matar dukan tsiya kuma ya umarci matansa su kashe ta
  • Alkalin kotun, Mai Shari'a Dakta Bello, ya baiwa wanda ake ƙara beli bisa wasu sharuɗɗa, sannan ya dage sauraron karar

Kano - Wani dattijo dan shekara 50, Ahmadu Muhammad, ya gurfana a gaban kotun shari'ar Musulunci, bisa zargin razana wata mata a jihar Kano.

The Nation ta rahoto cewa, Muhammad, wanda ke zaune a ƙauyen Zaidawa Fulani, karamar hukumar Ɗanbatta, ana tuhumarsa da laifin aikata laifin fin ƙarfi da kuma razanarwa.

Mai gabatar da ƙara daga hukumar yan sanda, Insufekta Abdul Wada, ya shaida wa kotun cewa wata mata mai suna, Hajara Umaru, daga Zaidawa Fulani, ita ce ta shigar da kara a ofishin CID, ranar 20 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wani mai Aski ya daba wa Dan Okada Sukuddireba har lahira kan gaddama

Kotun Musulunci
Magidanci ya lakadawa budurwa dukan tsiya, ya umarci matarsa ta kashe ta a Kano Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Me ya haɗa mutanen biyu?

Ya bayyana wa kotu cewa a wannan rana wata gardama ta haɗa Hajara da Muhammad, wanda ya kai ga yasa bulala ya zane ta kuma ya umarci matansa su kashe ta.

Mai gabatar da karar yace wannan laifi da ya aikata ya saba wa sashi na 266, 397, 165 da kuma 227 na kundin dokokin Fanal Code.

Amma a nasa bangaren, wanda ake ƙara, Ahmadu Muhammad, ya musanta duk tuhume-tuhumen da ake masa.

Wane mataki kotu ta ɗauka?

Alkalin kotun, mai shari'a Dakta Bello Khalid, ya baiwa mutumin da ake ƙara beli bisa sharaɗin gabatar da mutum biyu waɗan da za su tsaya masa.

Haka nan kuma, Dakta Bello, ya ƙara da cewa wajibi ne waɗan nan mutanen da za su tsaya masa ya kasance yan uwansa ne na jini.

Kara karanta wannan

Kotun Shari'a ta umarci mata ta tattara komatasanta ta bar gidan tsohon mijinta cikin sa’o’i 72 a Kaduna

Daga nan kuma, sai Alkalin ya ɗage sauraron karar har sai zuwa ranar 3 ga watan Fabrairu, na sabuwar shekara 2022.

A wani labarin na daban kuma Wani mutumi ya yi lalata da mata 10 a Otal da sunan Kwamishinan jiha

Yan sanda sun yi ram da wani mutumi bisa zargin amfani da sunan kwamishinan Akwa Ibom yana damfaran mutane.

Kakakin yan sanda na jihar, Odiko Macdon, yace wanda ake zargi ya kwanta da mata 10 bisa alkawarin zai taimaka musu su samu aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: