'Yan sanda sun kama wasu mutane 2 da suka kashe malamin addini suka sace kuɗinsa bayan ya basu masauki
- Yan sanda a jihar Legas sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargi da kashe wani faston cocin RCCG a Legas
- Mutanen biyu, Farouk Mohammed da Jamiu Kasali sun halaka faston ne sun tsere da jakar kudinsa bayan ya basu masauki a cocinsa
- Kasali da Mohammed sun bayyana cewa waka suka zo yi Legas amma suka canja shawara bayan sun ga malamin addinin da jakar kudi
'Yan sandan Jihar Legas, sun kama wasu mutane biyu, Farouk Mohammed da Jamiu Kasali da ake zargi da kashe wani Babatunde Dada, fasto na cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) a FESTAC Legas.
Kwamishinan yan sandan Jihar Legas, Hakeem Odumosu, ya tabbatar da kama Mohammed da aka bi sahunsa zuwa Ilorin, Jihar Kwara, shi kuma abokin laifinsa, Kasali, aka kama shi a FESTAC, Legas, Guardian ta ruwaito.
Odumosu ya ce an gano makamai da aka yi amfani da su wurin halaka faston yana mai cewa ba da dadewa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.
Idan za a iya tunawa an kashe faston ne ta hanyar daba masa wuka a ranar 2 ga watan Disamban 2021 sannan suka tsere da kudade masu yawa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
The Guardian ta gano cewa wadanda ake zargin da suka yi ikirarin su mawaka ne sun tafi cocin sun ce ba su da masauki a Legas hakan yasa faston ya taimaka musu.
An rahoto cewa wadanda ake zargin sun fito ranar Lahadi sun mika rayuwarsu ga Yesu a gaban al'umma.
Yadda suka halaka faston
Daya daga cikin wadanda ake zargin, Kasali, ya shaida wa manema labarai yadda faston ya ba su kudi da abinci a ranar da suka kai masa hari.
A cewarsa:
"Faston ya zo cocin da safe ya ba mu abinci ya kuma bamu kudi ya tafi. Daga bisani ya zo da jaka da kudi a cikinta.
"Bayan wasu awanni, an kira Farouk a waya an fada masa ya zo gida cikin gaggawa domin mahaifiyarsa bata da lafiya. Muna tunanin yadda za mu samu kudi don kai ta asibiti a lokacin da faston ya shigo da jakar kudin.
"Mun bi bayan faston muka buga masa katako a kansa, kafin muka caka masa kwalba a wuya. Ya fadi kasa, muka dauki jakar kudin muka tsere."
A bangarensa, Mohammed ya yi wa iyayensa karya cewa zai tafi Legas ne wani gasar waka.
Ya ce:
"Na yi wa mahaifiyata karya cewa zan tafi wata gasa inda zan samu a kalla N200,000. Mu mawaka ne masu tasowa. Mun shafe shekaru 3 muna waka, da abubuwa basu tafi yadda muke so ba, sai muka canja shawara.
"Mun shigo Legas ne domin mu yi waka. Amma muna ganin faston da kudin kawai sai muka canja shawara."
Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba
A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.
‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.
Asali: Legit.ng