Gwamnan APC ya rantsar da sabbin ciyamomi 35 da mutane suka zaba a jiharsa
- Gwamna Kayode Fayemi na jam'iyyar APC ya rantsar tare da jan hankalin sabbin ciyamomi 35 da mutane suka zaba a jihar Ekiti
- Fayemi ya roki su saka aikin al'umma, walwala da jin daɗin su a kan gaba fiye da abin da ransu ke so
- Sabbin shugabannnin sun nuna jin daɗin su tare da yaba wa gwamnan bisa nagarta da kyakkyawan jagorancinsa
Ekiti - Gwamnan jihar Ekiti, Dakta Kayode Fayemi, a ranar Talata ya rantsar da sabbin ciyamomi, da mataimakansu a kananan hukumomi 16 da kuma yankunan cigaba (LCDAs) 19 dake faɗin jiharsa.
Wannan na zuwa ne biyo bayan nasarar da suka samu a zaben kananan hukumomi da ya gudana ranar 4 ga watan Disamba, 2021, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Fayemi ya roki sabbin shugabannin su fifita tsaro da ayyukan al'umma fiye da abubuwan da suke so a ƙashin kan su.
Kazalika ya roke su da su yi amfani da damar da suka samu wajen magance rikice-rikice da tashe-tashen hankula a ciki da wajen yankunan su.
Wane ayyuka ya dace su yi wa mutane?
Gwamnan ya shawarci ciyamomin su kirkiri wasu tsare-tsare da ayyuka, waɗan da za su taimaka wa rayuwar al'ummarsu.
Dakta Fayemi yace:
"Ku yi aiki tare da hukumomi da ma'aikatun gwamnatin mu, domin ku saka yankunan ku a ayyukan da muka tanada domin karkara da sauran su."
"Ku nemo hanyoyin da zasu inganta samun kudin haraji a yankunan ku sannan ku tabbata kun toshe duk wata kafa ta zurarewar kuɗaɗen."
Bayan haka gwamnan ya bukaci sabbin shugabannin su yi aiki tare da hukumar tattara harajin cikin gida ta jiha domin tabbatar da an yi gaskiya.
Ciyamomi sun yaba wa gwamna
Shugaban ƙaramar hukumar Effon, Olabode Olatunji, wanda ya yi jawabi a madadin yan uwansa, ya yaba wa gwamnan bisa nuna halin dattako da nagarta.
Sannan ya jinjina wa gwamnan bisa kirkirar (LCDAs) domin ƙara matso da harkokin gwamnati kusa da al'umma.
A wani labarin na daban kuma Mambobin jam'iyyar PDP 4,000 zasu sauya sheka zuwa APC mai mulki a Jigawa
Jam'iyyar APC reshen jihar Jigawa dake Arewa maso yammacin kasar nan tace nan ba da jimawa ba zata karbi mambobin PDP 4,000.
Shugaban APC a Jigawa, Sani Gumel, yace masu sauya shekan sun ɗauki matakin dawowa APC ne saboda kyakkyawan jagoranci.
Asali: Legit.ng