Garkuwa da mutane: Dakarun ‘Yan Sanda sun kubutar da mutum kusan 100 daga jejin Zamfara
- Jami’an tsaro sun bada sanarwar ceto wasu Bayin Allah da suke tsare daga hannun ‘yan bindiga
- Mutane akalla 97 da suka shafe wata da watanni a hannun miyagu a jihar Zamfara sun samu ‘yanci
- A wata sanarwa da aka fitar yau, an tabbatar da cewa ana duba lafiyar wadanda aka ceto a asibiti
Zamfara - Jaridar Punch ta rahoto cewa jami’an tsaron sun kubutar da mutane 97 da suke tsare a kungurman jejin Arewa maso yammacin Najeriya.
A wani rahoto da ya fito a yau Talata, 4 ga watan Junairu, 2021, an ji mutanen da aka yi garkuwa da su watanni biyu da suka wuce, sun samu ‘yanci.
Punch tace Rundunar ‘yan sandan Najeriya suka bada wannan sanarwa dazu nan da yamma.
Hakan na zuwa ne bayan sojoji da ‘yan sanda su na ta kokarin bankado ‘yan bindigan da suka addabi Zamfara da sauran jihohin da ke makwabtaka.
Ana duba lafiyarsu
Mafi yawan wadanda aka ceto mutanen kauyuka da aka tsare, aka bukaci su biya kudin fansa. Yanzu haka kwararru su na duba lafiyarsu a asibitoci.
Mutane 68 a Shinkafi...
A wani kokari da jami’an tsaron suka yi a ranar Litinin, an ceto mutane 68 da aka tsare a gungun ‘yan bindiga a kauyukan da ke garin Shinkafi, Zamfara.
‘Yan sanda sun ce sun yi nasarar kubutar da wadannan mutane ne da taimakon wani tsohon ‘dan bindiga wanda yanzu ya tuba, ya na aiki da jami’an tsaro.
A sanarwar da ‘yan sanda suka fitar, daga cikin mutanen da aka ceto akwai mata, kananan yara har da maza da aka dauke su watanni uku da suka wuce.
...29 a jejin Tsafe
Jaridar PM News ta kawo labari cewa a wani kokarin da dakarun ‘yan sanda suka yi, sun ceto mutane 29 a dajin kuncin kalgo a yankin Tsafe, Zamfara.
Wadannan Bayin Allah da aka ceto a karamar hukumar ta Tsafe sun shafe kwanaki 60 a hannun ‘yan bindiga, sai yanzu Allah ya yi za su hada da iyalansu.
'Yan bindiga sun yi tsiya a Filato
A makon nan aka ji cewa ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban kungiyar ASUU a jami'ar jihar Filato da kuma wani tsohon ‘Dan takarar Gwamna.
Miyagun ‘Yan bindigan sun yi awon-gaba da jigon na PDP a Shendam, Hon. Kemi Nshe, sun bukaci a kawo N100m, daga baya sun rage kudin zuwa N50m.
Asali: Legit.ng