Ku yiwa 'yayanku tarbiyya bisa al'adunmu, Lai Mohammed ya yi kira ga iyaye

Ku yiwa 'yayanku tarbiyya bisa al'adunmu, Lai Mohammed ya yi kira ga iyaye

Ministan Labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya yi kira ga iyaye, makarantu da sauran masu ruwa da tsaki su zage dantse wajen yiwa yara kyakkyawan tarbiyya da zai saita rayuwansu.

Alhaji Lai ya bayyana hakan ne a taron haska Fim din “Death and the King’s Horseman”, a jihar Legas ranar Litinin, 3 ga Junairu, 2022, rahoton Punch.

Farfesa Wole Soyinka ne ya rubuta littafin “Death and the King’s Horseman”, kan abubuwan da suka faru a Najeriya lokacin mulkin mallaka.

A jawabinsa, Lai Mohammed yace:

"Mun san abinda fasahar zamani tayi mana. Mun san muhimmancinsa, amma wajibi ne mu tafiyar da shi tare da al'adunmu."
"Wajibi ne ku tarbiyyantar da yaranku koda yaushe kan muhimmancin al'adunmu."
"Wadannan al'adu ne zasu nuna banbanci tsakanin mutumin kirki da mara tarbiyya. Shi yasa akafi fi fyade da wasu laifika a kasashen yamma, saboda a nan akwai al'adu masu muhimmanci garemu."

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: ‘Yan gida daya su biyu sun nitse a ruwa a jajiberin sabuwar shekara

Lai Mohammed ya yi kira ga iyaye
Ku yiwa 'yayanku tarbiyya bisa al'adunmu, Lai Mohammed ya yi kira ga iyaye

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng