Yadda Marigayi Tofa ya jajirce domin hana a tsige Sanusi da kafa sababbin masarautu a Kano
- Tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi ta’aziyya na rashin dattijo kuma attajiri, Alhaji Bashir Tofa
- Khalifa Sanusi ya bayyana Marigayi Tofa a matsayin wanda ya tsaya domin kare martabar Kanawa
- Marigayin ya na cikin wadanda suka nemi su takawa Gwamna Ganduje burki kan raba masarauta
Kano - Bashir Othman Tofa ‘dan siyasa ne, kasurgumin attajiri wanda dukiyarsa ta taimaki al’umma, sannan kuma ‘dan kishin-kasa, baya ga haka dattijo.
A sakon ta’aziyyar da aka rubuta na rashin wannan dattijo a Daily Trust, an tuna da yadda ya dage domin nuna adawarsa ga yunkurin tarwatsa masarautar Kano.
Tsohon Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya bayyana Tofa a matsayin mutumin karshe da ya tsaya tsayin-daka domin kare Kanawa da kuma tarihinsu.
Muhammadu Sanusi II ya yabi dattijon da ya kare shi a lokacin da ake neman raba shi da gidan sarauta.
Kamar yadda ya saba fadawa masu iko gaskiya, Tofa bai ji dadin yadda gwamnar Abdullahi Umar Ganduje ya raba masarautar kasar Kano ta koma gidaje biyar ba.
Kokarin Advocates for A United Kano
Wannan Bawan Allah a karkashin kungiyar Advocates for A United Kano da yake jagoranta, ya yi tir da matakin da gwamnatin Kano ta dauka, yace ya saba doka.
Sauran 'yan kungiyar sun hada da Rt. Hon. Ghali Umar Na’Abba CFR, Farfesa Jibrin Ibrahim, Malam Abba Dabo, Aishatu Dankani mni MFR, da Lawal Audi.
Ragowar su ne Dr. Dalhatu Sani Yola, Amina BB Faruk, Bashir Yusuf Ibrahim, Malam brahim Ado-Kurawa, Dr. Bala Muhammad da kuma Farfesa Faruk Sarkin Fada.
Alhaji Bashir Tofa bai tsaya a kan magana ba kurum, ya shigar da karar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, ya na kalubalantar raba masarautar Kano da tayi.
Sai dai Marigayi Tofa bai yi nasarar hana gwamnati yin abin da tayi niyya ba. An sauke Sanusi II daga kan karaga bayan an kirkiri karin sababbin masaratu hudu.
Bashir Tofa ya tafi gidan da kowa zai je
A ranar Litinin aka tashi da labarin mutuwar Alhaji Bashir Othman Tofa. Dattijon ya rasu a ranar 2 ga watan Junairu, 2022 bayan ya yi fama da 'yar rashin lafiya.
Kun ji cewa a wata hira da ya yi ta karshe a Duniya, Marigayi Tofa ya koka cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta daukar shawara a kan batun tsaro.
Asali: Legit.ng