Idan Buhari na son zaman lafiya ya saki Nnamdi Kanu a shekarar nan, Ohaneaze Ndigbo
Kungiyar kare muradun kabilar Igbo a Najeriya, Ohanaeze Ndigbo ta lashi takobin kauraewa zaben 2023 muddin Shugaba Muhammadu Buhari bai saki Nnamdi Kanu a shekarar 2022 ba.
Kungiyar ta yi kira ga Shugaban kasan ya saki Nnamdi Kanu muddin yana son zaman lafiya ya dawo a yankin kudu maso gabas.
Kungiyar ta yi wannan kira ne a jawabin sabon shekarar da ta saki ranar Asabar ta hannun Sakataren Janar din ta, Okechukwu Isiguzoro.
A jawabin, ya bayyana cewa shi kanshi Buhari ya san sakin Nnamdi Kanu na da muhimmanci wajen wanzuwar zaman lafiya a yankin.
Yace:
"Shugaba Muhammadu Buhari ya taimaka ya saki Nnamdi Kanu a 2022 don samar da zaman lafiya, tsaro, da nutsuwa a yankin kudu maso gabashin Najeriya."
"Amma idan ba'a sakeshi a 2022 ba, kamar yadda shugabannin Arewa (Matasa ACF da Dattawan Arewa NEF) ke kira, babu zaben 2023 a gabashin Najeriya bisa ga dokar zaman gida da ake yi kuma hakan zai tsananta matsalar tsaro a kudancin Najeriya."
Buhari ya san muhimmancin sakin Nnamdi Kanu
Kungiyar ta bayyana cewa Shugaba Buhari ya san sakin Nnamdi Kanu zai taimaka wajen dawo da martabar Najeriya a idon duniya.
Hakazalika, Kabilar Igbo shirya take da mulkar Najeriya a 2023 don gyara kasar.
A cewar jawabin:
"Buhari ba zai iya kawar da kai daga sakin Nnamdi Kanu ba, zai taimaka wajen dawo da martabar Najeriya a idon duniya."
"A 2023 kuma, muna son shugaban kasa ya zama dan kablar Igbo saboda tabbatar da adalci da kuma biyayya ga yarjejeniyar da akayi na kama-kama a 1999."
Asali: Legit.ng