Kukah: Duk da yawan sukar da na ke yi wa gwamnatinsa, Buhari bai dena daukan waya na ba
- Rabaran Matthew Hassan Kukah, babban faston shiyyar Sokoto, ya ce duk da yawan caccakar gwamnatin shugaba Buhari da yake yi, amma shugaban bai daina daga wayarsa ba
- Bishop din yana cikin manyan masu caccakar gwamnatin shugaba Buhari wadanda su ka shahara saboda hakan, har zargin Buhari da rashin adalci wurin hukunci yayi
- Yayin tattaunawa da manema labarai a ofishin cocin Katolika ta St Bakhita da ke Sokoto a ranar Juma’a, Kukah ya ce alakar da ke tsakaninsa da Buhari ba ta lalace ba
Sokoto - Rabaran Matthew Hassan Kukah, Bishop din cocin Katolika da ke shiyyar Sokoto, ya ce duk da caccakar gwamnatin shugaban kasa Buhari, shugaban bai daina daga wayarsa ba, Daily Trust ta ruwaito.
Faston wanda yana daya daga cikin manyan masu caccakar gwamnati wanda ya yi hakan sau dayawa, ya taba zargin Buhari da rashin adalci ta hanyar fifita na kusa da shi.
Ya ce alakarsa da Buhari mai kyau ce
Yayin tattaunawa da manema labarai a ofishin cocin Katolika ta St Bakhita a ranar Juma’a, Kukah ya ce su na ci gaba da zumunci da Buhari.
Daily Trust ta bayyana yadda ya kara da cewa babu abinda ya fi daga masa hankali fiye da rashin tsaron da yake hauhawa da kashe-kashen ake yi a kasar nan, hakan ke sa ya caccaki gwamnati ba kawai tsana bace.
A cewarsa a kasashen da suka ci gaba idan mutum ya caccaki gwamnati yabonsa ake yi
Kamar yadda ya shaida:
“Idan na daga waya na kira shugaban kasa yanzun nan zai dauka. Akwai lokacin da na kira shi bai dauka ba amma daga baya sai da ya kira ni muka gaisa.
“A kasashen da suka ci gaba idan ka caccaki gwamnati yaba maka ake yi. Kalli yadda mutane su ke yabon marigayi Archbishop Desmond Tutu, amma anan da ka fadi gaskiya ka zama makiyin gwamnati.”
Kukah ya yaba wa yadda shugaban kasa ya ki amincewa da gyare-gyaren dokokin zabe, inda ya ce ya kamata a ba jam’iyyu damar zaben ‘yan takararsu da kansu don zabe.
Gwamna ya kori surukinsa daga aiki, ya umurci kwamishina ya maye gurbinsa
A wani labarin, Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya sanar da korar surukinsa, Mataimakin Manajan, Hukumar Kare Muhalli ta JIhar Abia, ASEPA, ta Aba, Rowland Nwakanma, a ranar Alhamis, The Punch ta ruwaito.
A cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jihar Abia, Barista Chris Ezem ya fitar, Ikpeazu ya kuma 'sallami dukkan shugabannin hukumar tsaftace muhalli a Aba amma banda na Aba-Owerri Road, Ikot Ekpene da Express.'
Amma gwamnan ya bada umurnin cewa dukkan 'masu shara ba a kore su ba, su cigaba da aikinsu na tsaftacce hanyoyi da tituna a kowanne rana.
Asali: Legit.ng