An daure ‘Dan Najeriya da yake aiki a asibitin kasar Amurka saboda laifin kwanciya da masu jinya
- Kotu ta samu wani mutumin garin Middletown da laifin kwanciya da marasa lafiya a kasar Amurka
- Wannan mutumi mai suna Godbless Uwadiegwu, ma’aikacin wani asibiti ne a yankin Warren County
- Asalin Godbless Uwadiegwu ‘Dan Najeriya ne, Alkali ya zartar masa da hukuncin daurin shekara uku
United States – Punch ta ce wani ma’aikacin lafiya a kasar Amurka, Godbless Uwadiegwu ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi na lalata da marasa lafiya.
Da ake shari’a da shi a kotu, Godbless Uwadiegwu ya yarda ya yi lalata da wasu mata a lokaci dabam-dabam, a asibitin da yake aiki a yankin Warren County.
Mista Uwadiegwu mai shekara 59 wanda yake zaune a garin Middletown, kasar Amurka, zai yi shekara uku a gidan yari kamar yadda Alkali Don Oda ya zartar.
Rahoton wlwt ya nuna a ranar Talata. 28 ga watan Disamba, 2021, Mai shari’a Oda ya yankewa wannan mutumi hukunci na daurin shekaru uku a gidan maza.
Wasu iyalan wadanda malamin jinya ya yi lalata da su, ba su halarci zaman kotun ba saboda rashin jiragen sama da ke yawo a dalilin dawowar COVID-19.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Erika Bourelle ta karanto wasiku a kotu
The Eagle tace sai dai wata mai kare hakkin wanda ake zargin an yi wa wannan aikin na masha’a, Erika Bourelle ta karanto wasikunsu a madadinsu.
A zaman da aka yi, Bourelle ta karanto wasikar wani daga cikin ‘ya ‘yan wata wanda wannan ma’aikacin asibiti ya yi lalata da ita, yayin da ba ta da lafiya.
Yaron yace Uwadiegwu ya rika kawowa mahaifiyarsu kyauta domin ta yarda da shi, daga nan shi kuma ya samu damar amfani da ita yayin da ta ke faman jinya.
"Ban manta abin da ya yi ba"
Wata wanda ke zargin Uwadiegwu ya kwanta da ita ba tare da izininta ba, ta fadawa kotu yadda wannan malamin asibiti ya yi amfani da ita a lokacin ta na jinya.
“Wasu ba za su tuna ba, amma ni zan tuna. Wannan ya faru da ni ne a ranar farko da na zo asibitin, zan kama ruwa, sai ya zo ya taimaka mani da tsumma.”
“Sai na ce Kai! Me ka ke yi haka?! Sai kuwa ya gigice, ya ce ‘yi hakuri, kuskure ne wannan.’ Ya kamata a yanke masa mafi munin hukunci a gidan yari.”
Sanusi II ya yi shekara 30 da aure
Kwanan nan aka ji cewa a shafinta na Twitter, Khadija Sanusi Lamido Sanusi ta kwarara addu’o’i na musamman na taya iyayenta cika shekaru 30 da auren juna.
A 1991 ne Mallam Muhammadu Sansu II ya auri Sadiya Ado Bayero, ya na shekara 30 a Duniya.
Asali: Legit.ng