Minista ya jero tulin nasarori 100 da Gwamnatin Buhari ta samu a Najeriya a shekarar 2021
- Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta jero irin nasarorin da ta samu a shekarar nan ta 2021
- Alhaji Lai Mohammed ya bayyana wadannan cigaba da aka samu ne a wajen taron ‘yan jarida
- Lai ya ce gwamnatin APC ta yi nasarar farfado da tattalin arzikin kasa da bunkasa sha'anin tsaro
Lagos - Mai girma ministan yaɗa labarai na kasa, Lai Mohammed, ya bayyana irin nasarorin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu a shekarar bana.
The Cable ta rahoto Alhaji Lai Mohammed a ranar Alhamis, 30 ga watan Disamba, 2021, ya kira taron manema labarai, inda ya fadi nasarorin da aka samu.
A cewar Ministan, duk da irin kalubalen rashin tsaro, gwamnatin APC ta yi kokari wajen yakar ta’adanci da farfado da tattalin arzikin kasar a shekarar nan.
“Abubuwan da muka yi shi ne mu tattaro manyan nasarorin da aka samu, shiyasa jerin yake da tsaro.”
“Mun kawo nasarori 100 da gwamnatin Buhari ta samu a shekarar 2021. Ba a auna nasara da kalubalen da aka fuskanta, sai dai yadda aka fuskance su.” - Lai
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wasu nasarori gwamnati ta samu a 2021?
Rahoton yace jerin ya fara ne da nasarorin da jami’an tsaro suka samu a kan ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’ddan da ke tada kayar-baya a wasu jihohin Najeriya.
Sai kuma ayyukan tituna da aka yi, daga ciki akwai hanyar Nnewi-Uduma, Kano-Maiduguri, Vandeikya-Obudu, da Sokoto-Tambuwal-Jega-Kontagora-Makera.
A cikin jerin akwai gadoji dabam-dabam; gadar Ikom, gadar iyakar Najeriya-Kamaru, da gadar Neja.
Ministan yace an kawo tsare-tsare da suka inganta tattalin arziki; samar da aikin yi, da farfado da harkar ma’adanai. Sannan an gyara wasu filayen jirgin sama.
Har ila yau, Lai ya ambaci nasarorin da aka samu a sha’anin noma da samar da ruwa. Manoma sun samu jarin miliyoyin kudi, an kuma ciyar da yaran makaranta.
Baya ga cigaba da aka gani wajen yakar rashin gaskiya a gwamnatin kasar, BBC ta rahoto Ministan yada labaran yace an fara wasu ayyukan titin jirgin kasa.
An kuma inganta yadda ake samun biza a Najeriya, sannan an gyara wasu gidajen yari. Sannan an ba matasa miliyan 1 aikin N-Power, an kuma dauki aiki a NNPC.
Masoyin Buhari ya yi ridda
Sirajo Saidu Sokoto ya na cikin masu ba gwamnatin Muhammadu Buhari kariya a dandalin Facebook, amma da alama ya iso tashar karshe a a motar Buhariyya.
Wannan mutumi yace tun da har ‘yan bindiga suka dauke ‘yanuwansa sai da aka biya kudin fansa, ba a taimaka masa ba, to ya koma goyon bayan Kwankwasiyya.
Asali: Legit.ng