Nasara daga Allah: Gwarazan yan sanda sun damke kasurgumin dan binidga da ya addabi Zamfara, sun ceto mutane

Nasara daga Allah: Gwarazan yan sanda sun damke kasurgumin dan binidga da ya addabi Zamfara, sun ceto mutane

  • Hukumar yan sanda ta sanar da cewa jami'anta sun samu nasarar kama kasurgumin dan bindiga, Sani Mati Mai Yan Mata
  • Kwamishinan yan sandan jihar, Ayuba Elkana, yace ɗan bindigan ya shiga hannu ne yayin da suke kan hanyar kai hari da tawagarsa
  • Yace jami'ai sun kwato mutum 10 daga cikin mutanen da aka sace a garin Gada, karamar hukumar Bundugu

Zamfara - Rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara ta bayyana cewa jami'ai sun samu nasarar cafke kasurgumin ɗan bindiga, Sani Mati Mai Yan Mata.

Da yake jawabi ga manema labarai a hedkwatar yan sanda, kwamishinan yan sanda na jihar Zamfara, Ayuba Elkana, yace jami'ai sun cafke Mai Yan Mata ne yayin da ya jagoranci tawagarsa za su kai hari.

Kara karanta wannan

An damke wani matashin dan bindiga yana kokarin tare hanya, an ceto mutum 10 daga hannunsa

Premium Times ta rahoto cewa Mai Yan Mata ya shiga hannu ne yayin da yake kan hanyar zuwa toshe hanya a kauyen Kukiya domin sace matafiya.

Yan sanda
Nasara daga Allah: Gwarazan yan sanda sun damke kasurgumin dan binidga da ya addabi Zamfara, sun ceto mutane Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Kwamishinan ya kara da cewa an kama shi da bindiga kirar AK-47 da kuma alburusai da mashin Boxer da sauran wasu makamai.

Mati wanda aka fi da Mai Yan Mata, jagoran yan bindiga ne da ya addabi yankin Zurmi - Shinkafi na jihar Zamfara, a cewar Elkana.

A baya-bayan nan wasu yan bindiga da suka kai hari garin Gada, dake karamar hukumar Bungudu, sun kashe basarake da wasu mutane, sannan suka yi awon gaba da mutane.

Yan sanda sun kubutar da mutane

A cewar kwamishinan yan sandan, jami'an sa sun samu nasarar ceto mutum 10 daga cikin mutanen da aka sace a Gada.

Kara karanta wannan

Hotunan mai jinyan da ya sace motar Asibiti a jihar Kano bayan Yan sanda sun damkeshi

Mista Elkana yace:

"Nan take aka haɗa tawaga da ta haɗa da yan sanda, sojoji da yan sa'kai suka bi bayan yan bindigan kuma suka samu nasarar kubutar da waɗan da suka sace."

CP Elkana yace tuni aka haɗa mutanen da iyalansu, kuma daga cikin su har da jariri ɗan wata ɗaya da kuma mahaifiyarsa.

A wani labarin na daban kuma Gwamna a Najeriya ya bayyana yadda aka kama shi da mahaifinsa kan zargin kisa

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike , ya bada labarin yadda rikicin mukami a kauyensu ya yi sanadin kama shi, mahaifinsa da sauran iyalan gidan su.

Gwamnan yace a rayuwarsa baki ɗaya ba zai taba mantawa da Lauya Ukala ba, wanda shi ne ya tsaya musu a wannan lokaci har gaskiya ta yi halinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262