Da Dumi-Dumi: Buhari ya amince a ɗauki ƙarin 'yan sanda 10,000 aiki a Najeriya
- Shugaba Muhammadu Buhari ya dauki matakin rigakafin dakile karuwar rashin tsaro da ke adabar sassan Najeriya
- A cewar Buhari Sallau, Shugaban na Najeriya ya amince a dauki sabbin jami'an yan sanda guda 10,000 a kasar
- Tuni dai an tuntubi wadanda abin ya shafa bayan fara aikin daukan sabbin 'yan sandan a sassan Najeriya daban-daban
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a dauki sabbin jami'an yan sanda 10,000 daga jihohi 36 da babban birnin tarayya, Abuja.
Buhari Sallau, hadimin shugaban kasar ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 29 ga watan Disamba, cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook.
A cewarsa, an zabi mutane 10 daga kowanne karamar hukuma 774 a kasar, ya kara da cewa za a yi aikin daukan sabbin yan sandan ne a sassa daban-daban a kasar.
Sallau ya kara da cewa tuni an tuntubi mutanen da suka yi nasara ta hanyar tura musu sako ta adireshin imel da suka yi amfani da shi a lokacin da suke rajista.
Daukan aiki: Rundunar yan sanda ta fitar da sanarwa mai muhimmanci ga masu son shiga aiki
Tunda farko, Legit.ng ta rahoto cewa shirin na gwamnatin tarayya na kara yawan yan sanda a kasar da ake yi a halin yanzu na shiga wani sabon mataki.
Rundunar yan sandan ta sanar da cewa za a yi gwaji ga wadanda suka yi nasarar samun aikin a 2020.
Sanarwar da ta fito ta bakin mai magana da yawun yan sandan Legas, CSP Adekunle Ajisebutu ta ce za a yi gwajin ne a ranar Juma'a 29 da Asabar 30 ga watan Oktoba.
Ajisebutu ya ce za a yi gwajin na Legas ne a cibiyar gwaji na WAEC da ke Ogba.
Ku saurari karin bayani ...
Asali: Legit.ng