Yadda masu rike da madafan iko suka taka mai tsaron Buhari a Aso Villa da gidan 'Yan Sanda

Yadda masu rike da madafan iko suka taka mai tsaron Buhari a Aso Villa da gidan 'Yan Sanda

  • An gano abin da ya sa aka yi wa kwamishinan ‘yan sanda, Abdulkarim Dauda ritaya kwatsam kwanan nan
  • CP Abdulkarim Dauda shi ne babban jami’in da ke kula da tsaron shugaba Muhammadu Buhari a Aso Villa
  • Bayan sabanin da ya samu da masu iko, an janye karin matsayin da aka yi masa, aka kuma yi masa ritaya

Abuja - Sababbin bayanai sun fito daga Daily Trust a kan abin da ya sa aka janye karin matsayin da aka yi wa kwamishinan ‘yan sanda, Abdulkarim Dauda.

Majiyoyi dabam-dabam sun shaidawa jaridar cewa Abdulkarim Dauda ya na cikin wadanda hukumar ‘yan sanda ta karawa matsayi zuwa matakin AIG.

Daga baya sai aka ji cewa an cire sunan babban jami’in da ke kula da tsaron shugaban kasa (CPSO), daga wadanda za a nada a matsayin mataimakan sufeta.

Kara karanta wannan

Buhari zai iya kawo karshen ta'addanci kafin cikar wa'adin mulkinsa, Femi Adesina

Ganin hakan, CP Dauda wanda ‘da ne a wajen shugaban kasa, ya rubuta takarda, ya na neman a kyale shi ya zama AIG, ya bada uzuri a kan aikin da aka sa shi.

Laifin me Dauda ya aikata?

Abin da ya jawo aka hana yi wa Dauda karin matsayin shi ne wasu manya na jin haushin yadda ya goyi bayan Aisha Buhari a rikicin da aka yi kwanaki a Aso Villa.

'Yan Sanda
CSO CP Dauda a Aso Villa Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Dauda wanda kanin Mamman Daura ne ya samu matsala da hadimin shugaban kasa, Sabiu Yusuf wanda ya samu sabani da Aisha Buhari a lokacin annobar COVID-19.

Bayan wannan abin ya faru, sai aka cire kwamishinan ‘yan sandan daga aikin gadin shugaban kasa, aka maida shi ya zama shugaban makarantar ‘yan sanda a Kaduna.

Kara karanta wannan

Minista ya tona asiri, ya ce Jonathan bai bar wa Buhari komai a asusun Najeriya ba

Halin da CP Dauda yake ciki

A baya, Sufetan ‘yan sanda, Mohammed A. Adamu ya karawa Dauda wa’adin shekaru uku a aiki, don haka aka ce zai yi ritaya a 2023 duk da ya cika shekara 60.

A makon da ya gabata ne kwamishinan yada labarai na hukumar PSC, Austin Braimoh, ya bada sanarwar cewa an janye karin wa’adin da aka yi wa Dauda a aiki.

Austin Braimoh yace hukumar ta ‘yan sanda ta gano an saba doka a karin girman da aka yi wa babban jam’in, don haka aka yi masa ritaya a matakin kwamsihina.

Bugu da kari, an bukaci Dauda ya dawo da duk albashin da ya karba tun daga 2020 zuwa yau.

Manjo Hamza Al-Mustapha ya yi magana

Tsohon Dogarin Janar Sani Abacha ya jefi manyan masu kudin Najeriya, da wadanda aka ba damar hako ma’adanai da zargin hannu a matsalar rashin tsaro.

A ra’ayin Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya), dole sai an yi da gaske kafin a iya dawo da kasar nan daidai domin manyan masu kudi na tada kayar-baya.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya gana da kamfanin Jamus kan yadda za a bullowa aikin jirgin Maradi-Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng