Hotunan mai jinyan da ya sace motar Asibiti a jihar Kano bayan Yan sanda sun damkeshi

Hotunan mai jinyan da ya sace motar Asibiti a jihar Kano bayan Yan sanda sun damkeshi

  • Wani mai jinyar daurin karaya a kafa ya sace motar asibiti a wani kauye a garin Dawakin Tofa, Kano
  • Jami’an ‘yan sanda sun gano wannan motar daukar marasa lafiya da mutumin da ya sace a jihar Jigawa
  • Hukumar ta bayyana shi gaban yan jarida gabanin gurfanar da shi gaban kotu

Jami'an Hukumar yan sandan jihar Kano sun cika hannu da wani mai jinya, Saminu Sa’idu, wanda ya sace motar daukan marasa lafiya a asibitin da aka kwantar da shi.

Jami'an yan sandan sun bayyanashi ga al'umma da motar da ya sace.

Zaku tuna cewa wannan mai jinya da ya sace motar asibiti ya na fama da daurin karaya a kafa.

Jaridar Aminiya ta rahoto cewa wannan abin ban mamaki da takaici ya faru ne a garin Kano.

Kara karanta wannan

An damke wani matashin dan bindiga yana kokarin tare hanya, an ceto mutum 10 daga hannunsa

‘Yan Sanda sun yi nasarar damke wannan barawo da ya sace motar daukar marasa lafiya a kauyen Takwasa, karamar hukumar Babura, jihar Jigawa.

Ana zargin wannan mutumi da sungume motar daukar marasa lafiya da gawa, tattare da duk wasu magungunan da ake ajiyewa a cikinta saboda larura.

Hotunan mai jinyan da ya sace motar Asibiti a jihar Kano
Hotunan mai jinyan da ya sace motar Asibiti a jihar Kano bayan Yan sanda sun damkeshi Hoto: Leadership
Asali: Facebook

Hotunan mai jinyan da ya sace motar Asibiti a jihar Kano bayan Yan sanda sun damkeshi
Hotunan mai jinyan da ya sace motar Asibiti a jihar Kano bayan Yan sanda sun damkeshi
Asali: Facebook

Hotunan mai jinyan da ya sace motar Asibiti a jihar Kano bayan Yan sanda sun damkeshi
Hotunan mai jinyan da ya sace motar Asibiti a jihar Kano bayan Yan sanda sun damkeshi
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: