Ta kacame tsakanin 'yan siyasar Zamfara bayan 'yan daba sun hargitsa taron PDP

Ta kacame tsakanin 'yan siyasar Zamfara bayan 'yan daba sun hargitsa taron PDP

  • 'Yan jam'iyyar PDP a jihar Zamfara karkashin Mahadi Ali-Gusau, sun zargi jam'iyyar APC da hargitsa musu taron su na zaben shugabanni
  • Mabiyan Mahadi sun bayyana cewa, Gwamna Matawalle da mabiyansa tsoron su suke yi bayan su ne suka kai shi inda yake
  • Sai dai jam'iyyar APC ta musanta zargin inda tace dama tun farko an san PDP da rikicin cikin gida, don haka lamarin cikin gida ne

Gusau, Zamfara - Magoya bayan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Mahadi Ali-Gusau, sun zargi shugabannin jam'iyya mai mulki a jihar da shirya farmakin da aka kai wurin taron jam'iyyar na safiyar Litinin.

Premium Times ta ruwaito cewa, 'yan daban sun kutsa wurin taron jam'iyyar PDP a Samaru da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara. 'Yan daban sun lalata wurin da aka shirya domin taron.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi magana a kan cafke sirikin tsohon gwamna a wurin Ibada

Ta kacame tsakanin 'yan siyasar Zamfara bayan 'yan daba sun hargitsa taron PDP
Ta kacame tsakanin 'yan siyasar Zamfara bayan 'yan daba sun hargitsa taron PDP. Hoto daga Premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jami'an tsaro ne suka kai tallafi kafin 'yan daban su bar wurin kuma a cigaba da taron inda aka tsara, Premium Times ta ruwaito.

A wata takarda da aka fitar bayan taron, Aminu Gyangyam, babban sakataren mataimakin gwamnan, ya ce jam'iyyar APC a jihar ta na tsoron jam'iyyar PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce jam'iyya mai mulki a jihar da Gwamna Bello Matawalle suna yin abubuwa tamkar yara ga jam'iyyar adawa.

"Suna tsoron jam'iyyar PDP kuma sun yarda cewa hanya daya ta bayyana tsoron shi ne su lalata taronmu, kuma kun dai gani da kanku sai da muka yi taron kuma muka fitar da shugabannin jam'iyya.
“Gwamna Matawalle ya sani cewa, wannan jam'iyyar ce ta kai shi inda ya ke yanzu kuma bai dace wannan ya zama irin sakayyar da za ka yi wa jam'iyyar."

Kara karanta wannan

Labari cikin Hotuna: Yan daba sun kai hari filin gangamin taron jam'iyyar PDP a Zamfara

Gyangyam ya ce jam'iyyar ta yi zaben shugabannin ta cike da nasara kuma suna kirga kwanakin da suka rage kafin su turgude jam'iyyar a jihar.

A yayin martani kan zargin, tsohon kakakin Gwamna Matawalle, wanda shi ne sakataren yada labaran jam'iyya mai mulki a jihar, Yusuf Idris, ya ce abinda ya faru lamarin cikin gida ne.

Kamar yadda yace, tun a farko dama PDP jam'iyya ce mai rikicin cikin gida, babu ruwan jam'iyya mai mulki da fadansu.

Mawaki ya gwangwaje shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, da wakar yabo da jinjina

A wani labari na daban, wata waka ta kwarzantawa tare da yaba wa fitaccen dan bindiga, Bello Turji, tana yawo a halin yanzu a arewacin Najeriya cikin mutanen da suke fama da cin zarafi tare da rashin kwanciyar hankalin da 'yan bindigan suke saka yankin.

Turji, wanda dan asalin garin Shinkafi ne daga jihar Zamfara, shi ne shugaban 'yan ta'addan da ke addabar jihohin Sokoto, Zamfara da wani sashi na jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnoni 6 suka hana Majalisa juyawa Shugaban kasa baya a kan kudirin gyara zabe

'Yan ta'addan ke da alhakin kisa da hana daruruwan jama'a sakat a yankin, Premium Times ta ruwaito.

Daya daga cikin mummunan al'amari shi ne kisan ranar 6 ga watan Disamban shekarar nan inda 'yan ta'addan suka kone mota cike da fasinjoji da ke kan hanyar su ta zuwa karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng