Nasara daga Allah: Sojoji sun ragargaji 'yan ISWAP a Yobe, sun kama da dama sun hallaka 7
- Wasu mayakan ISWAP sun yi yunkurin yiwa garin Buni Yadi da ke jihar Yobe kawanya amma ba su yi nasara ba
- Sojoji da taimakon ‘yan banga sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan, inda suka kame biyar tare da fatattakar sauran
- A cewar majiyoyin leken asiri, sojojin sun aika a kalla bakwai daga cikin maharan zuwa kabarinsu yayin wannan mummunan hari
Yobe - A ranar Lahadi, 26 ga watan Disamba ne mayakan ISWAP suka kaddamar da hari a garin Buni Yadi dake karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe, amma sojojin Najeriya sun fatattake su.
Bukar Bulama, wani mazaunin garin Buni Yadi, ya shaidawa jaridar TheCable cewa mafarauta ne suka taimaka wa sojojin a yayin wannan mummunan hari.
A cewarsa, sojojin sun kama biyar daga cikin maharan tare da kwato wata motar sulke ta 'yan ta'addan.
Bulama ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Babu wani mazaunin Buni Yadi da ya samu rauni ko kuma ya mutu saboda jami'an tsaro sun kai musu dauki kafin faruwar lamarin."
Yadda aka afkawa garin Buni Yadi
Jaridar PR Nigeria ta bayyana cewa, maharan sun afkawa garin ne da misalin karfe 5 na yamma cikin gungun 'yan ta'adda har biyu.
Daya daga cikin gungun ya kai harin ne kan ‘Charly Company’, yayin da daya kuma suka yi yunkurin kai hari a makarantar sojoji na musamman a yankin.
Daya daga cikin majiyoyin leken asirin ya bayyana cewa:,
"'Yan ta'addan sun yi amfani da shanu ne a matsayin garkuwa domin samun saukin shiga ba tare da an gane su ba, amma sojoji sun gano mugunyar shirinsu da dabarunsu, inda nan take suka yi musu ruwan alburusai."
Majiyar ta ce an kashe bakwai daga cikin maharan yayin da sojojin suka ci karfinsu.
Buni Yadi dai ta zama yankin da ke fama da rikici ne a shekarar 2014 bayan da mayakan Boko Haram suka kashe dalibai maza 58 na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke garin.
A wani labarin daban, Sojojin Najeriya sun kama wani kasurgumin shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB a jihar Enugu.
Jaridar Punch ta rahoto cewa sojoji sun fatattaki mazauna a yankin Akpawfu da ke karamar hukumar Nkanu ta gabas a jihar Enugu.
An tattaro cewa sojojin sun shiga unguwar ne a ranar 24 ga watan Disamba, yayin da mazauna Akpawfu ke gudanar da bukukuwan jajibirin Kirsimeti.
Asali: Legit.ng