Babu kanta yayin da ‘Yan bindiga suka dauke Mai daki, 'ya ‘yan ‘Dan Sanda a jajibirin Kirismeti
- Wani ‘Dan Sanda ya na cikin wadanda aka yi wa ta'adi a harin da ‘Yan bindiga suka kai a garin Zaria
- A daren kirismeti ne wasu ‘Yan bindiga su ka shigo birnin Zazzau, suka yi garkuwa da wasu mutane
- Rahotanni sun ce miyagun ‘Yan bindigan sun hada da Mata da ‘Ya ‘yan jami’in ‘Dan Sanda a Wusasa
Kaduna - Rahotanni mabambanta sun tabbatar da cewa an dauke akalla mutane shida a yankin Wusasa, garin Zaria, jihar Kaduna a daren bikin kirismeti.
A wani rahoto da ya fito daga jaridar Daily Trust a ranar 26 ga watan Disamba, 2021, an ji cewa har da iyalin wani jami’in tsaro a cikin wadanda aka dauke.
Baya ga matar wannan jami’in ‘dan sanda, ‘yan bindigan sun hada da wasu ‘ya ‘yansa ‘yan mata. Baya ga haka kuma an yi nasarar yin gaba da mutum hudu.
Da kimanin karfe 10:30 na daren ranar Asabar, miyagun ‘yan bindiga suka shigo garin Wusasa, suka rika bi gida zuwa gida domin su dauke Bayin Allah.
Dakarun Kaduna State Vigilance Service, KADIVS, sun yi kokarin kawowa agaji, amma lokacin da suka isa wurin, an riga an dauke wadannan mutane shida.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Yayin da jami’an KADIVS suka iso, sun rika barin wuta da ‘yan bindigan. Miyagun sun tsere da wadanda suka dauke, daga baya aka gane gudaje uku aka shiga.”
- Majiya
An bar mutane da alhini ana bikin kirismeti
Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa an saci mutanen ne daga gidaje uku a yankin na Wusasa.
Yayin da yanzu mutane suke yin bikin kirsmeti, miyagun ‘yan bindigan sun bar wadannan iyalai da daukacin al’ummar Wusasa da Zaria cikin halin dar-dar.
A rahoton da ya fito daga Daily Post, an ji cewa an yi yunkurin tuntubar kakakin ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, amma ba a same shi ba.
A ‘yan kwanakin nan, ‘yan bindiga sun addabi garuruwan jihar Kaduna. Ana yawan tare titin Kaduna-Abuja da na Zaria-Kaduna, domin a sace mutane.
Zargin da Ameh Ebute ya ke yi wa Gwamnoni
Kwanan nan aka ji Sanata Ameh Ebute yana cewa wasu ‘Yan siyasa sun yi taron-dangi, sun taso Muhammadu Buhari a gaba tun da ya zarce a kan mulki a 2019.
Ameh Ebute wanda ya rike Majalisar Dattawa a shekarar 1993 yace gwamnatin APC tayi kokarin samar da zaman lafiya da tsaro, amma ana mata zagon-kasa.
Asali: Legit.ng