Mutum 7 sun rasa rayukansu a mumunan hadarin da ya auku ranar Kirismeti
- Wani mumunan hadarin mota ya auku ranar Asabar, 25 ga Disamba, a babban titin Sagamu-Ore dake jihar Ogun
- Rahotannin sun nuna cewa an yi rashin rayuka akalla bakwai yayinda fasinjoji da dama suka jigata
- Sakta Kwamanda na hukumar FRSC ya tabbatar da aukuwar hadarin ta bakin jami'ar wayar da kai, Florence Okpe
Sagamu, Ogun - Akalla rayuka bakwai sun salwanta yayinda wasu suka jigata a wani mumunan hadarin motan da ya auku ranar Kirismeti a jihar Ogun.
Daily Trust ta ruwaito cewa wata mota kirar Mercedes Benz MarcoPolo ta yi hadari ne a titin Sagamu-Benin-Ore da cikin daren Asabar misalin karfe 12:00.
A cewar rahoton, motar ta tashi daga Ojuelegba da Legas kuma ta nufi kudu maso gabas.
Jami'ar wayar da kan jama'a a hukumar kiyaye hadura FRSC, Florence Okpe, ta tabbatar da aukuwar lamarin a jawabin da ta saki.
Okpe tace mutum 63 ke cikin motar; maza 40, mata 15 da yara takwas.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Me ya haddasa hadarin?
Jami'ar ta bayyana cewa motar ta kwacewa direban ne yayinda yake kokarin wuce wata motar ba bisa tsari ba.
Okpe tace:
"An duba lafiyar wadanda suka jikkata yayinda aka ajiye gawawwakin wadanda suka mutu a dakin ajiyan gawan asbitin jihar dake Ijebu Ode."
"An tuntubi ofishin yan sandan Odogbolu kuma an mika musu motar da tayi hadari don dauketa daga hanya."
Asali: Legit.ng