Shehun Borno: Tsaro ya inganta kwarai a Jihar Borno karkashin mulkin Buhari
- Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn-Umar Elkenemi, ya ce tsaro ya gyaru a jihar Borno tun bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau mulki
- Shehu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da shugaban kasa ya je jihar don yin taron kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar Borno ta yi
- A cewarsa, wajibi ne su yi godiya bisa yadda zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa ya samu a cikin jihar tare da yankin arewa maso gabashin Najeriya
Borno - Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn-Umar Elkenemi, ya ce matsalolin tsaro sun gyaru kwarai a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar, Vanguard ta ruwaito.
Shehu ya yi wannan furucin ne a ranar Alhamis yayin da shugaban kasa ya je jihar don kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar Borno ta yi.
A cewar Shehu kamar yadda Vanguard ta ruwaito:
“Muna farin cikin sanar da shugaban kasa cewa a hankali zaman lafiya ya samu a jihar Borno kuma wajibi ne mu yaba wa kokarin mulkinka akan kawo zaman lafiya mai dorewa a wannan jiha da kuma yankin arewa maso gabas.
“Ina farin cikin sanar da shugaban kasa cewa yanzu haka an ci gaba da noma a wurare daban-daban na jihar kuma ‘yan gudun hijira da dama sun koma yankunan su.”
Shehu ya yaba akan yadda ‘yan Boko Haram su ka dinga tuba
Shehun ya nuna jindadinsa akan yadda ‘yan Boko Haram da dama su ka dinga tuba kuma ya ce akwai sa ran nan ba da jimawa ba kasar gaba daya ta dawo daidai.
Ya yaba akan jajircewa sojojin Najeriya wanda bisa kokarinsu yasa jihar ta samu zaman lafiya da tsaro tare da yiwa iyalan wadanda su ka rasa rayukansu sakamakon sadaukarwa ga kasar su ta’aziyya.
Kamar yadda yace:
“A bangarenmu, ba za mu daina addu’o’i ba akan nasarar kawo zaman lafiya da su ka yi a kasar nan ba kuma lallai shugaban kasa duk da kalubale, ya samu nasarori a bangarori daban-daban ba tattalin arzikin Najeriya.
“Ga gwamna Babagana Zulum kuwa, sai dai mu yi masa fatan Allah ya kara masa karfi da jajircewa don duk da matsalolin tsaro ya ci gaba da kokarin gyara jihar wanda mutane da dama su ka amfana da shi.”
Shehun ya bukaci shugaban kasa ya yi gyara a wasu titina
Shehu ya nemi shugaban kasa ya sa hannu akan gyare-gyaren wasu titina musamman na Damboa-Biu titin Gamborun Ngala, Biu-Shani da Kukawa sai kuma Kukawa zuwa Gazamala har Damasak ta Gashagar zuwa Malam Fatori.
Ya ce gyaran titinan ba tsaro kadai zai gyara ba har taimakawa zai yi wurin bunkasa anguwannin da su ka samu barakar tattalin arziki.
A bangaren gwamna Zulum kuwa ya nuna farincikinsa akan nasarorin da suka samu inda yace idan ba don sojojin Najeriya ba da sauran jami’an tsaro, da ba a shawo kan ta’addancin yankin ba.
Gwamnan ya ce a hankali matsalolin tsaron yankin su na ta raguwa a jihar.
Asali: Legit.ng