Gwamna ya kori surukinsa daga aiki, ya umurci kwamishina ya maye gurbinsa

Gwamna ya kori surukinsa daga aiki, ya umurci kwamishina ya maye gurbinsa

  • Okezie Ikpeazu, Gwamnan Jihar Abia ya sallami surukinsa, Rowland Nwakanma, daga aiki a matsayin mataimakin manajan hukumar kare muhalli ta jihar Abia, ASEPA, ta Aba
  • Gwamna Ikpeazu ya umurci kwamishinan muhalli na jihar Abia, Sam Nwogu ya karbi ragamar shugabancin hukumomin tsaftacce muhalli na Aba
  • Hakazalika, ya umurci kwamishinan nan take ya tallata guraben aiki domin a maye gurbin surukinsa da wasu da aka sauke daga mukaminsu

Jihar Abia - Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya sanar da korar surukinsa, Mataimakin Manajan, Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Abia, ASEPA, ta Aba, Rowland Nwakanma, a ranar Alhamis, The Punch ta ruwaito.

Gwamna ya kori surukinsa daga aiki, ya umurci kwamishina ya maye gurbinsa
Gwamna Ikpeazu ya kori surukinsa daga aiki, a umurci kwamishina ya maye gurbinsa. Hoto: The Punch
Asali: UGC

A cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jihar Abia, Barista Chris Ezem ya fitar, Ikpeazu ya kuma 'sallami dukkan shugabannin hukumar tsaftace muhalli a Aba amma banda na Aba-Owerri Road, Ikot Ekpene da Express.'

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan da ya yi shekara 8 a mulki ya fashe da kuka ya na jawabi wajen jana'iza

Amma gwamnan ya bada umurnin cewa dukkan 'masu shara ba a kore su ba, su cigaba da aikinsu na tsaftacce hanyoyi da tituna a kowanne rana.

Ikpeazu ya nada Sam Nwogu ya shugabanci hukumomin tsaftacce muhalli

Ikpeazu ya kuma umurci Kwamishinan Muhalli, Sam Nwogu ya karbi ragamar shugabancin hukumomin tsafacce muhalli a yankin. Gwamnan ya umurci kwamishinan ya 'tallata guraben aiki na neman kwararrun masu ilimin tsaftacce muhalli a yankunan' nan take.'

Gwamnan ya yi gargadin cewa:

"Daga yanzu, ba za a amince da sakaci ba a hukumar tsaftace Aba da Umuahia, kuma nan take yana bukatar a kwashe dukkan shara da bola da ke biranen Aba da Umuahia ba tare da bata lokaci ba."

A farkon wannan watan, an tsige shugaban ASEPA, Honarabul Eze Okwulehie daga mukaminsa cikin kasa da awanni biyu saboda tsokacin da aka ruwaito ya yi a gidan rediyo.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya tura sako ga 'yan Kaduna, ya ce su gaggauta cika shirin tallafin Korona

Okwulehie ya shaida wa gidan rediyon cewa hukumomin da abin ya rataya a kansu ba su bada kudaden da hukumar ta nema ba domin ayyukanta.

Ba za ta saɓu ba: Za mu hukunta doddani da ke cin zalin jama'ar mu, Gwamnatin Abia

A wani labarin, gwamnatin jihar Abia ta umarci kama duk wani dodo tare da gurfanar da shi matsawar aka kama shi da cutar da mazauna da baki a jihar yayin shagalin kirsimeti da sabuwar shekara, The Nation ta ruwaito.

Sakataren gwamnatin jihar, Chris Ezem, a wata takarda ya ja kunnen dodanni akan dakatar da titina da ababen hawa, inda yace matsawar aka kama zai fuskanci fushin shari’a.

Gwamnatin jihar Abia ta ce ta dauki matakin ne don tabbatar da tsaro ga rayuka da dukiyoyin al’umma yayin shagulgulan da ke karatowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164