Innalillahi: Babbar Motar Dakom Gas Ta Bi Ta Kan Jama'a da Dama Yayin da Birkinta Ya Makale a Ibadan
- Wata babban motar dakon Iskar Gas ta kucce wa direba ta hallaka mutane da dama a Ibadan, babban birnin jihar Oyo
- Wani mutumi a wurin da hatsarin ya faru ya tabbatar da lamarin, wanda ake tsammanin birkin motar ne ya ki ci, yasa ta yi kan mutane
- Rundunar yan sanda reshen jihar Oyo ta tabbatar da faruwar lamarin, amma tace ba ta da alƙaluman waɗan da hatsarin ya shafa
Ibadan, Oyo - Wata babbar motar dakon iskar Gas ta yi ajalin mutane da dama a shataletalen Makola dake Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Daily trust ta rahoto cewa birkin motar ne ya ƙi kama wa yayin da ɗireban ke kokarin kwana a sanannen shataletalen Makola, sakamakon haka ta kashe mutane da dama.
Wata majiya a wurin da hatsarin ya faru, ta tabbatar wa wakilan mu cewa mutane da dama sun rasa rayuwar su.
Majiyar tace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Eh dagaske hatsarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Na takaice muku zance akwai wani jariri ƙarami da ya rasa idanuwansa biyu a hatsarin."
"A halin yanzu da nake magana da ku, sun ɗauke wasu gawarwaki daga wurin, amma har yanzun muna da ragowar gawar mutum biyu a nan."
Shin yan sanda sun san da lamarin?
Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Oyo, Adewale Osifeso, ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Haka nan kuma ya yi alkawarin zai bincika domin ya gano bayanai kan hatsarin, sannan ya dawo ga wakilan mu.
A wani labarin na daban kuma Gwamna Masari ya sha alwashin kawo karshen ta'addancin yan bindiga a arewa kafin dauka mulki a 2023
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina yace zasu haɗa karfi su murkushe yan bindiga a jihohin arewa da abun ya shafa kafin wa'adin mulkinsu ya ƙare a 2023.
Gwamnan, wanda ya faɗi haka yayin rattaba hannu kan kasafin kudin 2022 ranar Laraba a Katsina, yace ba gudu ba ja da baya a yaƙi da ayyukan yan bindiga.
Asali: Legit.ng