El-Rufai ya tura sako ga 'yan Kaduna, ya ce su gaggauta cika shirin tallafin Korona

El-Rufai ya tura sako ga 'yan Kaduna, ya ce su gaggauta cika shirin tallafin Korona

  • Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya nemi 'yan jiharsa da su cika wani shirin tallafin gwamnati na Korona
  • Ya ce shirin zai taimakawa mutane da dama a jiharsa, inda ya bayyana kananan hukumomin da za su mora
  • Ya kuma yi bayanin yadda za a nemi wannan tallafi cikin sauki, tare da fadan yadda shirin yake tafiya

Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi kira ga daukacin mazauna kananan hukumomi tara da unguwanni 42 a jihat da su yi rajistar shiri Rapid Response Register (RRR) na gwamnatin tarayya.

RRR shiri ne na tallafin gwamnatin tarayya da aka kirkira don rage munanan radadin Korona a cikin birane da talakawan birni, musamman masu karbar albashi na yau da kullum wadanda kullen annobar ya shafa.

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai
El-Rufai ya tura sako ga 'yan Kaduna, ya ce su gaggauta cika shirin tallafin Korona | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

El Rufa'i wanda ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, ya ce tsarin rajistar abu ne mai sauki, domin kawai lambobin USSD (*969#) za a danna a wayar hannu.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: An bindige manoma 45 har lahira a Nasarawa, wasu 5,000 sun rasa muhallinsu

Kananan hukumomin da suka cancanci a kason farko sun hada da: Birnin Gwari, Chikun, Kudan, Zaria, Kaura, Igabi, Sanga, Jema’a, Kagarko, Lere, Kachia, Soba, Giwa, Zangon Kataf, Ikara, Kajuru da Kauru.

Gwamnan ya ce za a samar da takamaiman lambobin kowace unguwa a cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

El-Rufai ya kuma yi karin haske inda yace za a iya kiran 969 domin karin bayani da sanin lambobin kowace unguwa.

Ya kara da cewa, a karkashin shirin za a ba 'yan jihar N5,000 duk wata na tsawon watanni shida.

El Rufa'i ya yi alkawarin cewa, Kaduna State Social Investment (KADSIO), ta hanyar Kaduna State Operations Coordinating Unit (KADSOCU), za ta fara wayar da kan jama'a a kananan hukumomin a 'yan makonni masu zuwa.

Hakazakika, sanarwar ta bayyana wasu lambobin wayan hannu da 'yan jihar za su iya kira don samun karin bayani daga hukumomin gwamnatin jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun hallaka mutane tare da kone gonakai

Kalli bidiyo da sanarwar:

'Mu aika su lahira su hadu da Allah' - El-Rufai ya ce bai san wani zancen tubabbun 'yan ta'adda ba

A wani labarin, Nasir El-Rufai, gwamnan Jihar Kaduna ya ce, bai yarda da tsarin sauya wa 'yan ta'adda hali ba, ya kara da cewa hanyar da ta fi dace wa a bi da su kawai shine su 'tafi su gamu da Allah'.

Gwamnan ya bayyana matsayarsa kan batun ne a ranar Talata yayin da ya ke zantawa da manema labarai a gidan gwamnati bayan ganawa da Shugaba Muhamamdu Buhari, The Cable ta ruwaito.

Ya kai ziyara gidan gwamnatin ne domin yi wa Shugaba Buhari bayani kan harin baya-bayan da yan ta'adda suka kai inda suka kashe mutum 40 a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.