Yanzu-yanzu: Yan Majalisar Wakilai sun amince da Kasafin Kudin 2022, sun kara N700bn
- Bayan watanni biyu suna tattauna a kai, yan majalisar wakilai sun amince da daftarin kasafin kudin 2022
- Yan majalisan sun yi wasu sauye-sauye cikin abinda Shugaba Buhari ya gabatar a kasafin
- Daga ciki akwai karawa wasu ma'aikatu kudi da kuma kiyasin farashin danyen man fetur
Abuja - Majalisar wakilan tarayya a ranar Talata, 21 ga Disamba 2021, ta amince da daftarin kasafin kudin 2022 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabata mata a watan Oktoba.
Maimakon N16.39tr da Buhari ya gabatar, yan majalisan sun kara sama da bilyan 700 kai zuwa N17.126 trillion.
ChannelsTV ta ruwaito cewa majalisar ta kara N400bn wa ma'aikatu irinsu INEC, Majalisar dokoki da ma'aikatar tallafi da jin kai, dss.
Majalisa kuma ta kara kiyasin farashin danyen mai daga $57/ganga zuwa $62/ganga.
Yan majalisan kuma sun ce hukumar EFCC da NFIU su rika amfani da kashi 10% na kudaden suka kwato don karfafa yaki da rashawa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Asali: Legit.ng