Wanda ya yi wa Buhari Minista a 1984 ya kawo shawarwarin yadda za a magance rashin tsaro

Wanda ya yi wa Buhari Minista a 1984 ya kawo shawarwarin yadda za a magance rashin tsaro

  • Tsohon Ministan harkokin gida, Mohammed Magoro yace za a iya shawo kan matsalar rashin tsaro
  • Janar Mohammed Magoro (mai ritaya) ya ba gwamnatin shugaba Buhari wasu muhimman shawarwari
  • Tsohon Sojan yace dole a magance matalsar rashin aikin yi, kuma a nemi gudumuwar kasashen waje

Tsohon Ministan harkokin cikin gida a gwamnatin sojan Muhammadu Buhari, Manjo-Janar Mohammed Magoro ya yi magana a kan batun rashin tsaro.

A ranar Litinin, 20 ga watan Disamba, 2021, jaridar Vanguard ta rahoto Manjo-Janar Mohammed Magoro (mai ritaya) ya na maidawa shugaban PDP martani.

Mohammed Magoro yace babu dalilin da zai sa a gagara kawo karshen matsalar Boko Haram da ‘yan bindigan da suke satar Bayin Allah, a cikin watanni shida.

Buhari ya taba yin wannan a da - Magoro

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta jero tulin nasarorin Shugaba Buhari yayin da ya cika shekara 79

A shekarar 1983, lokacin Shehu Shagari yana mulki, ‘yan ta’adda suka addabi Najeriya a yankin tafkin Chadi, shugaba Buhari ya na GOC na runduna ta 3 a Jos.”
“A wannan lokaci ya maida rundunarsa Maiduguri, kuma ya yi kaca-kaca da ‘yan ta’addan. Yau ba GOC ba ne shi, shugaban kasa ne, ba mu sa ran ganin ya gaza.”
- Mohammed Magoro

Mohammed Magoro
Janar Mohammed Magoro Hoto; vanguardngr.com
Asali: UGC

Sarakuna za su iya taka rawar gani

Tsohon sojan ya bayyana cewa masu sarautar gargajiya za su iya taka rawar gani wajen magance wannan matsala, domin sun fi kusa da mutane da kan iyakoki.

Emergency Digest ta rahoto Magoro ya na cewa harshe daya ake amfani da shi a iyakokin kasar Benin zuwa Kamaru, don haka sarakuna za su iya bada gudumuwa.

Kara karanta wannan

Yanzu sai mun hada da noma da tuka motar haya, sannan mu koshi – ASUU tace gari ya yi zafi

Mohammed Magoro ya bada shawarar a kafa wata majalisa ta jami’an tsaro da samun bayanan sirri a karkashin sarakuna domin a shawo kan matsalar tsaron.

Inda matsalar ta ke, da kuma mafita

A jawabin na sa, Janar Magoro yace babban abin da yake jawo ta’addanci shi ne yawan matasan da ke zaman banza, don haka ya bada shawarar kafa kamfanoni.

Idan ana bukatar kamfanoni su yi aiki da kyau, dole a samu tituna da hanyoyin ruwa ko dogo da za a iya daukar kaya cikin sauki, kuma a samar da wutar lantarki.

Wata matsala da ake fuskanta a cewar sa shi ne karancin sojoji, sannan ya bada shawarar Najeriya ta hada-kai da Rasha da Sin domin samun kayan yaki.

Agwam Bajju ya kwanta dama

Da ake batun sarakuna, a jiya ne aka ji labarin mutuwar Agwam Bajju, Bayan tsawon lokaci ya na ta fama da rashin lafiya, Sarkin mai daraja ta daya ya rasu a Kaduna.

Kara karanta wannan

Farin jinin Shugaba Buhari ya yi mummunan sauka bayan hare-hare da kashe-kashe a Arewa

Mai martaba Nuhu Bature wanda shi ne Sarkin farko a kasar Zonkwa ya rasu a ranar Asabar. Bature ya fi shekara 25 ya na sarautar mutanensa a kudancin Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng