Wata soja ta gamu da fushin gidan soja yayin da ta amince za ta auri dan bautar kasa

Wata soja ta gamu da fushin gidan soja yayin da ta amince za ta auri dan bautar kasa

  • Rundunar sojin Najeriya ta tsare wata soja da ta amince da auren wani dan bautar kasa a sansanin NYSC da ke Kwara
  • Hakan ya biyo bayan ganin bidiyo da hotunan lokacin da ta amince da soyayyarsa a kafafen sada zumunta
  • Rundunar soji ta bayyana hakan ya saba wa dokokin gidan soja, kuma ta ce za ta dauki mataki a kai

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da tsare wata Soja da ta amince da bukatar auren wani dan bautar kasa a sansanin NYSC da ke Kwara.

Bidiyon masoyan da ke yawo an ga lokacin da suke abubuwan karbar soyayyar juna, lamarin da ya haifar da cin kalamai iri-iri a dandalin sada zumunta.

Shugaban hafsun soji, Janar Faruk Yahaya
Wata soja ta gamu da fushin gidan soja yayin da ta amince za ta auri dan bautar kasa | Hoto: thecable.ng
Asali: Facebook

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar soji Onyema Nwachukwu ya aika wa TheCable Lifestyle a ranar Lahadi, ya ce sojar dai ta karya wasu ka’idojin gidan sojoji.

Kara karanta wannan

Nasara: Sojoji sun ragargaji sansanin dan bindiga Bello Turji, sun hallaka da dama

Da yake bayyana dalilin tsare ta, jaridar Punch ta rahoto Nwachukwu na cewa wasu laifukan da ta aikata sun hada da kulla alaka a yayin da take bakin aiki da kuma tsundumawa soyayya a lokacin da take sanye da kayan aiki.

Kakakin rundunar ya kara da cewa dabi'ar sojar ya saba wa tsarin da ya dace da kuma tsarin aikin soja.

A cewar rundunar, idan da soja namiji ne ya aikata haka, da jama’a za su fassara hakan da cewa yana amfani da kakinsa ne wajen kulla alakar soyayya da 'yan bautar kasa da ke karkashin kulawarsa.

A cewar sanarwar:

“Soja macen da ake magana a kai ta keta dokokin NA. 1. Kulla alaka yayin da take bakin aiki a sansanin NYSC. Wato, yin mu'amalar soyayya da wanda ake horarwa."

Kara karanta wannan

Alkali ya fallasa lauyan da yayi yunkurin ba shi cin hanci a Plateau

“2. Dole ne jami'i ya yi aiki na tsawon shekaru 3, kafin ya sami damar yin aure 3. Ta bijirewa umarnin rundunar sojojin Najeriya kai tsaye da kuma umarnin yin amfani da kafofin watsa labarai.
"4. Shagaltuwar soyayya a lokacin da take cikin kaki. 5. Abin da ta aikata ya kasance abin kyama ga kyakkyawan tsari da horon soja.
"Duk abubuwan da ke sama, idan sun tabbata sun saba wa dorewa dokoki tare da ladabtarwa da abubuwan hukunci. A matsayinta na jami'ar soja, aikinta shi ne horar da ’yan bautar kasa ba wai ta yi cudanya da wani daga cikinsu ba.
“An samar da wadannan ka’idoji ne da nufin samar da ingantaccen shugabanci da kuma ladabtar da Sojoji. Abin tambaya anan shine, idan soja namiji ne fa? Ta yaya jama'a za su fahimci matakin?
“Tabbas, da an yi la’akari da cewa yana cin gajiyar wata 'yar bautar kasa ne, wacce ake horarwa, a karkashin kulawarsa.

Kara karanta wannan

Mawaki ya gwangwaje shugaban 'yan bindiga, Turji, da wakar yabo

"Hakanan batun yake a wannan lamarin. Sojojin Najeriya, kamar sauran sojoji, suna da ka’idojin ladabtarwa, sabanin na sauran jama'a gama gari. Kowane jami'i ya amince da kansa don bin wadannan ka'idojin doka."

Bayan auren mata biyu masu juna biyu, ango ya ji dadin zama dasu, ya ce dole ya yi kari

A wani labarin na daban, wani wanda ya auri mata biyu a rana guda mai suna Prince Erere Nana ya shawarci maza da su auri mata fiye da daya, matakin da ya ce zai dakile magudi a gidan aure.

Mutumin dan Najeriya daga kauyen Orhokpokpor da ke Delta ya jawo cece-kuce a intanet bayan sanar da gayyatar daurin aurensa inda ya bayyana cewa zai auri mata biyu masu juna biyu.

Da yake magana a wajen rufe bikin aurensa na gargajiya da matansa, Erere ya shaida wa BBC News Pidgin cewa shi ne mutumin da ya fi kowa farin ciki a duniya.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar tattali za ta sa rashin biyan haraji ya kai mutum kurkuku na tsawon shekara 5

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.