Da Dumi-Dumi: Jami'an kwastam sun damke babbar kwantena maƙare da makamai a Legas

Da Dumi-Dumi: Jami'an kwastam sun damke babbar kwantena maƙare da makamai a Legas

  • Yayin da lamarin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a Najeriya, jami'an kwastam sun yi babban nasarar dakile yunkurin shigo da makamai
  • Jami'an kwastam na Tin Can a Legas sun yi ram da wata kwantema makare da katan-katan na bindigu
  • A halin yanzun jami'ai na cigaba da bincine don gano alkaluman kayan dake ciki da kuma wasu bayanai

Lagos - Jami'an hukumar kwastam (NCS) na rundunar tashar jiragen ruwa Tin Can Island, sun kama wata babbar kwantena 1x40ft ɗauke da makamai.

Daily Trust ta rahoto cewa ana zargin mamallakin kwantenan ya bayyana cewa talabijin ɗin Plasma ne a cikin kwantenar tasa.

Sai dai da jami'an kwastam suka bincika sai suka gano cewa kwantenan na ɗauke da katan katan na bindigu ne a ciki.

Makamai
Da Dumi-Dumi: Jami'an kwastam sun damke babbar kwantena maƙare da makamai a Legas Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wata majiya ta shaida ma wakilan dailytrust cewa kwantenar ta samu ƙarin jami'in da ya tantance ta, wanda ya sa aka fara ɗora alamar tambaya kan jami'in farko.

Kara karanta wannan

Mai Hijabi, Shatu Garko, ta lashe gasar Mace mafi kyau a Najeriya 'Miss Nigeria' na bana

Kakakin jami'an kwastan na Tin Can, Mista Uche Ejesieme, ya tabbatar da lamarin da cewa kwantenar bindigun ta shiga hannu ne yayin gudanar da bincike na biyu.

Yace:

"Jami'ai sum kama kwantena maƙare da makamai, amma a halin yanzun mun nemi a kai ta sashin zartar da doka domin bincika ta sosai, mu gano alƙaluman abinda ke ciki da wasu bayanai."

Wane mataki za su ɗauka?

Ya ƙara da cewa, bisa dokokin hukumarsu, za su fara sanar da hedkwatar kwastam ta ƙasa dake Abuja, bayan kammala bincike 100% kan kwantenan.

"Wannan dalilin ne yasa ba mu sanar a hukumance ba, a yanzu da muke magana, ba mu da cikakken bayani kan wanda ya shigo da ita, daga ƙasar da da fito, da kuma yanayin bindigun."

Kara karanta wannan

Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika

"Amma zamu san wannan baki ɗaya da zaran jami'ai sun kammala bincike a kai."

Bugu da ƙari, hukumar kwastam ta sha alwashin gudanar da binciken kwakkwafi kan lamarin tun daga tushe da kuma kame duk me hannu, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

A wani labarin na daban kuma Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, Ya faɗi babban matsalar da zata hana zaben 2023

Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya yi gargaɗin cewa matukar ba'a shawo kan matsalar tsaro ba, babban zaben 2023 ba zai yuwu ba.

Jega yace wajibi a tunkari tsaron kasar nan dagaske, idan kuma ba haka ba babu jam'iyyar da zata amince da zaɓen 2023 da zaa gudanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262