Hukuncin kotu: Ku kwantar da hankulanku, Ganduje ya yi kira ga mabiyansa
- Kotun tarayya sake tabbatar da shugabannin jam'iyyar APC na Kano tsagin Sanata Ibrahim Shekarau
- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa wannan rikicin cikin gida ne kuma babu bukatar tada hankali
- Kotun ta jadadda cewa tsagin Sanata Ibrahim Shekarau da suka zabi Harun Zago a matsayin shugabansu na halatattun shugabanni
Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga mabiyansa mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) su kwantar da hankulansu bisa hukuncin kotu.
Ganduje yace mutan jihar su kasance cikin zaman lafiya ba tare da tada tarzoma ba.
Wannan ya bayyana a jawabin da Kwamishanan Labaran jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya saki da yammacin Juma'a.
Kotu ta tabbatar da tsagin Shekarau matsayin sahihan shugabannin APC a Kano
Wata babbar kotun tarayya dak zamanta a birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin Mai Sharia Hamza Muazu ta tabbatar da tsagin Shekarau ta gudanar da zaben shugabannin jam'iyyar APC a Kano.
Yayin Shari'a ranar Juma'a, Alkalin ya yi watsi da karar tsagin Ganduje kuma ya ci su tarar milyan daya kan batawa kotu lokaci.
Kotu ta tabbatar da cewa zaben da tsagin Shekarau tayi shine daidai kuma shugabanninsu ne shugabannin APC a jihar.
Ganduje ya umurci jami'an tsaro su yi aiki
Gwamnan yace tun da wannan siyasar cikin gida ne, Gwamnatinsa da jam'iyya zata nemo mafita.
Ganduje ya bukaci jami'an tsaro kada su lamunci wani ya tada zaune tsaye sakamakon wannan hukuncin.
Asali: Legit.ng