Ba zan daina muku aiki ba har sai ranar da na sauka a 2023: Buhari a jawabin cikarsa shekaru 79
- Shugaba Buhari ya yiwa yan Najeriya alkawarin cewa ba zai daina musu aiki ba har sai lokacin da ya sauka a 2023
- Shugaban kasan yace wa'adinsa na karewa a Mayun 2023 zai sauka kuma ya koma gonarsa dake Daura
- Buhari yayi wannan jawabi ne a birnin Istanbul yayin murnar cikarsa shekaru 79 a duniya
Istanbul, Turkiyya - Shugaba Muhammadu Buhari yayi bikin murnar cikarsa shekaru 79 a birnin Turkiyya ranar Juma'a, 17 ga watan Disamba, 2021.
Manyan hadimansa da Ministoci sun shirya masa bikin bazata karkashin jagorancin Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama.
Mamaki bisa abinda suka yi, Buhari ya yi alkawarin cewa ba zai daina yiwa Najeriya aiki da kokari ba har sai ranar da ya sauka daga karaga mulki.
Mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.
Yace:
"Na yi tunanin tunda ba na Abuja zan tsira daga wannan abu. Ina sa ran komawa gona ta a gida idan na sauka a 2023."
"Amma kafin lokacin, zan cigaba da iyakan kokari wajen yiwa kasar nan da al'ummarta aiki kamar da kundin tsarin mulki ya tanada."
Dirarsa ke da wuya, Shugaba Buhari ya gana da Shugaban kasar Turkiyya
Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, da safiyar Juma’a, 17 ga Disamba, 2021 a birnin Istanbul.
Hadimin Shugaban Kasan, Buhari Sallau, ya bayyana hakan a hotunan da ya saki a shafinsa na Facebook.
Shugabannin kasashen biyu sun yi zaman diflomasiyya tare Istanbul.
Wannan ganawa ya faru ne bayan da ya dira tashar jirgin birnin Istanbul.
Asali: Legit.ng