An karrama dan Najeriyan da mayar da kudi N11m da ya tsinta a Dubai

An karrama dan Najeriyan da mayar da kudi N11m da ya tsinta a Dubai

  • Wani matashi dan Najeriya wanda ya mayar da kudi 100,000 AED (N11,166,682.37) da aka manta a motarsa ya samu lambar yabo
  • Matashin mai suna Abraham Airaodion, ya samu karramawa ne daga kamfanin da yake yiwa aiki bisa gaskiyarsa
  • Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu kan wannan lamari inda wasu suka rika tambaya shin an bashi kudi?

Wani matashi dan Najeriya Abraham Airaodion, ya samu karramawa bisa gaskiyarsa bayan mayar da kudi 100,000 AED (N11,166,682.37) da wani fasinja ya manta da su cikin motarsa na Tasi.

Duk da cewa ba'a bayyana lokacin da abin ya auku ba, @instablog9ja ta ruwaito cewa kamfanin Tasin birnin Sharjah ta karramashi ranar Litinin, 13 ga Disamba, 2021.

An karrama dan Najeriyan da mayar da kudi N11m da ya tsinta a Dubai
An karrama dan Najeriyan da mayar da kudi N11m da ya tsinta a Dubai Hoto: Instablog9ja
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Waiwaye a 2021: Haziƙan Ɗaliban Najeriya 4 Da Suka Karya Tarihin Da Ba a Taɓa Zaton Wani Zai Iya Ba

Hotunan da aka daura kan IG sun suna lokacin da Abraham ya karbi takardar shaidar karramawar dauke da sunansa.

Yan Najeriya da dama sun tofa albarkatun bakinsu kan al'amari.

Kalli hotunan:

Jawaban makarantanmu:

Salis Bn Abdallah yace:

"Anfada musu baba buhari yayi yaki da cin hanci da rashawa to ga misalinan anfara gani gaskiya mu yan Nigeria munyi sa ar shugaba. Har a Manta Kudi kimanin miliyan 11 sannan a miyar gaskiya dole a jinjina maka dan Nigeria."

Mohammed Abubakar yace:

"Gskya yayi kokari
Duk da cewa.ba ruwanshi da mulkin manjo"

Mustapha Muhammad yace:

"Aiko Yayi Asara Awannan Yanayinda Ake Cikin Tab. Ai kawai Idan Kudinka ya Fadi to Dama Ba Rabonka bane Idan Kuma Na Tsinta To Dama Rabona ne"

Amadu Habu Gamawa

"Wannan gaskiya ne Allah ya qaramar imani"

Aliyu Muazu

"In ya koma gida sai yaci certificate din"

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng