Sabuwar dokar tattali za ta sa rashin biyan haraji ya kai mutum kurkuku na tsawon shekara 5

Sabuwar dokar tattali za ta sa rashin biyan haraji ya kai mutum kurkuku na tsawon shekara 5

  • Gwamnatin tarayya ta shigo da wani sabon kudiri na gyara tattalin arziki watau Finance Bill 2021
  • Wannan kudiri zai kawo wasu gyare-gyare a Najeriya idan aka yi nasara ya zama dokar gwamnati
  • Gyaran da za a gani sun hada da hukuma za ta iya bincike, ta daure wanda ya yi gaba da kudin haraji

Abuja - Gwamnatin tarayya na so a yanke hukuncin dauri a gidan yari da/ko tarar Naira miliyan biyar ga duk wani jami’i da aka samu da laifin cin haraji.

Jaridar Tribune tace gwamnatin tarayya ta kawo shawarar a garkame duk wani ma’aikaci da aka samu ya karkatar da kudin harajin da ya karba a gidan yari.

A dokar kasa, babu wanda ya isa ya taba harajin da aka tara da sunan gwamnati, ba tare da izinin majalisar tarayya ba, don haka ake neman a karfafa dokar.

Kara karanta wannan

Yanzu kam lokaci ya yi da ya kamata kowa ya nemi makami, gwamna Masari ya magantu

Cikin gyare-gyaren da sabon kudirin zai yi idan ya zama doka shi ne kara adadin harajin da ake karba a hannun kamfanoni idan suka samu ribar akalla N500m.

Baya ga haka za a fara karbar haraji daga kamfanonin caca da na mai da gas da sauransu. Ana sa ran hakan ya taimakawa gwamnati da samun kudin-shiga.

Shugaban kasa
Shugaban kasa Buhari a ofis Hoto: @GarShehu
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

FIRS za ta fara hukunta masu laifi

Idan kudirin ya zama doka a Najeriya, hukumar FIRS za ta samu damar karbar kudin Nigeria Police Trust Fund Levy, kuma ta iya hukunta kowane mai laifi.

Hukumar za ta dauki mataki a kan wadanda suka hana a duba na’urorinsu, ko bankunan da suka ki sauke nauyin harajin da yake kansu, ko masu kin biyan haraji.

Laifuffukan da hukumar FIRS za ta samu damar hukuntawa sun hada da tserewa da takardun haraji. Duk wanda aka kama da laifi zai yi shekara biyar a daure.

Kara karanta wannan

Jaruma Rahama Sadau ta caccaki gwamnatin Buhari kan hauhawar rashin tsaro

Sannan kudirin ya yi gyara a kan dokokin QCE na karbar harajin kanana da sababbin kamfanoni ta yadda za a guji tatsar kudin da za su iya hana kamfanonin cin riba.

An rahoto Ministar kudi, tattali da kasafin arziki, Zainab Ahmed ta na yi wa ‘yan majalisa bayani a kan wannan sabon kudiri da ake nema ya zama dokar kasa.

Kudirin Biodun Olujimi ya bar majalisa

A jiya ne aka ji yadda sabanin addini ya tilasta yin waje da kudirin daidaita maza da mata a dokar kasa. Sanata Biodun Olujimi ta kawo wannan kudirin a majalisa.

Manyan Sanatocin Arewa sun mike, sun ce wannan kudiri ya sabawa addinin musulunci. An samu Sanatocin kudu da suka nuna cewa su na goyon bayan haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng