Da duminsa: Shugaba Buhari da uwargidarsa zasu tafi kasar Turkiyya yau Alhamis
Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi birnin Istanbul, kasar Turkiyya ranar Alhamis, 16 ga Disamba, 2021 don halartan taron hadin kan Afrika da Turkiyya karo na uku.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana a jawabin da ya saki da safiyar nan.
Shugaban kasan zai samu rakiyar manyan ministoci da ma'aikatan gwamnati sama da guda goma.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Garba Shehu yace:
"Shugaba Muhammadu Buhari ranar Alhamis zai tafi Istanbul daga Abuja, don halartan taron hadin kan Turkiya da Afrika karo na uku, wanda Shugaban Recep Tayyip Ergogan, ya shirya."
"Ana kyautata zaton wannan taro zai samar da hanyoyin habaka hadin kai tsakanin kasar da kasashen nahiyar Afrika a shekaru biyar masu zuwa."
Ya kara da cewa Shugaban kasa zai samu rakiyar matarsa, Aisha Buhari; Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya); Ministan Abuja, Mohammed Bello da Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire.
Sauran sune Ministan Noma, Mohammed Abubakar; Ministan kasuwanci da masana'antu, Adeniyi Adebayo; NSA Babagana Monguno da Dirakta Janar na NIA, Ambasada Ahmed Rufa'i Abubakar.
Shugaban kasan zai dawo Abuja ranar Lahadi, 19 ga Disamba, Garba Shehu ya kara.
Asali: Legit.ng