Da Duminsa: An Kama Ɗan Sandan Najeriya Da Aka Gani Ya Yi Tatil Da Giya Ya Bugu a Wani Bidiyo
- Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta kama wani Sajan din ‘yan sanda, Onatunde Joba, bisa zarginsa da rashin da’a da rashin daraja
- Jami’in hulda da jama’an rundunar, SP Yemisi Opalola, ya ce har ranar Laraba ana ci gaba da tuhumarsa
- Bidiyon Sajan din ya yadu ne a kafafen sada zumunta inda aka gan shi ya yi mankas da giya wanda hakan ke nuna bai san mutuncin kansa ba
Jihar Osun - Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta kama wani sajan da ke karkashin rundunar, Onatunde Joba bisa zarginsa da rashin da’a, The Nation ta ruwaito.
An gan shi a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta a bige ya yi tatil da giya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yanzu haka ana ci gaba da tuhumarsa
Jaridar The Nation ta rahoto cewa jami’in hulda da jama’an rundunar, SP Yemisi Opalola, ya ce har yanzu ana kara tuhumarsa.
Opalola ya shaida cewa:
“Rundunar ‘yan sandan jihar Osun a kokarinta na kawar da dabi’un banza, rashin sanin darajar aiki da rashin dabi’u masu kyau, ta kama wani dan sanda, Sajan Onatunde Joba wanda bidiyonsa yayin da ya yi shaye-shaye ya yadu.
“Tuni hukumar ta ci gaba da bincike akan sa.”
Rundunar ba za ta lamunci rashin da’a ba
Ya kara da cewa:
“Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olawale Olokode, ya na amfani da wannan damar wurin daukar matakai akan rashin da’a ga duk wani ma’aikaci mai irin halinsa.”
Rundunar ta ce ba za ta lamunci rashin tarbiyya da zubar da mutunci ba daga wani jami’inta ko kuma mai kokarin shiga rundunar ba.
Kano: Ƴan Sanda Sun Kama Sojan Bogi, Zailani-Ibrahim Da Ya Ƙware Wurin Tatsar Masu Keke Napep
A wani labarin daban, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar damkar sojan bogi wanda ya kware wurin damfarar masu Napep, The Nation ta ruwaito.
Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abdullahi Kiyawa ne ya tabbatar da kamen a wata takarda wacce ya ba manema labarai ranar Talata a Kano.
A cewarsa, wanda ake zargin, Abubakar Zailani-Ibrahim, mai shekaru 27 ya gabatar wa da ‘yan sandan ofishin Rijiyar Zaki kansa a matsayin soja kuma ya je da wani mai Napep.
Asali: Legit.ng