Fadar shugaban kasa ta kashe N34bn na abinci da tafiye-tafiye a cikin shekaru 6

Fadar shugaban kasa ta kashe N34bn na abinci da tafiye-tafiye a cikin shekaru 6

  • Kamar yadda kasafin kudin Najeriya ya nuna, fadar shugaban kasa ta kashe kudi har N34bn na abinci da tafiye-tafiye a cikin shekaru shida
  • Sai dai kasafin kudin cin abinci da tafiye-tafieyn ya kunshi kayan abinci, cefane sannan kuma na tafiyan ya hada da tafiye-tafiyen cikin gida da na ketare
  • Shekarun da aka kwashe ana kashe wadannan makuden kudin sun fara tun daga shekarar da shugaba Buhari ya hau mulki zuwa wannan shekarar

Kasafin fadar shugaban kasa na abinci da tafiye-tafiye na tsawon shekara shida ya kai kudi har N34 biliyan kamar yadda aka gano bayanai daga kasafin kudi na gwamnatin tarayya.

Jimillar N5.16 biliyan kan abinci da N28.9 biliyan kan tafiye-tafiye, Punch ta ruwaito hakan.

Kasafin kudin da aka ware wa abinci ya kama daga kayan abinci, cefane, lemuka, gas na girki da sauransu, yayin da kudaden tafiye-tafiye suka hada da tafiye-tafiye na cikin gida da kasashen ketare.

Kara karanta wannan

Farin jinin Shugaba Buhari ya yi mummunan sauka bayan hare-hare da kashe-kashe a Arewa

Fadar shugaban ta kashe N34bn na abinci da tafiye-tafiye a cikin shekaru 6
Fadar shugaban ta kashe N34bn na abinci da tafiye-tafiye a cikin shekaru 6. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

A ranar 7 ga watan Oktoban 2021, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2022 ga majalisar dattawa da ta tarayya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kasafin kudin da ya kai N16.39tn zai cilla gwamnatin tarayya wurin aro N6.23tn.

Punch ta ruwaito cewa, an samu hawa da saukan kasafin kudi na tsawon lokaci.

A cikin lokutan da aka duba, kudin da aka ware na tafiye-tafiye ya kwashe da yawa daga cikin kasafin.

A shekarun 2016, 2017, 2018 da 2019, an ware zunzurutun kudi har N3.27bn, N3.12bn, N3.82bn da N3.39bn.

A 2016, abinci ya kwashe N518.45bn yayin da kudin tafiye-tafiye suka lashe N2.7bn.

A 2017, an samu ragowa a kudin abinci inda ya kwashe N681.79 miliyan yayin da kudin tafiye-tafiye ya kwashe N2.43bn.

Amma kuma a 2018, abinci ya kwashe N582.75m yayin da N3.23bn ya kare a tafiye-tafiye.

Kara karanta wannan

Ahmad Lawan ya bude sirri, ya fadi albashin sanataoci da 'yan majalisun Najeriya

A shekarar 2019, abinci ya kwashe N617.45m yayin da N2.98bn ta kwashe a tafiye-tafiye.

Jimillar kasafin kudi na abinci da tafiye-tafiye na shekarar 2020, 2021 da 2022 sun kai N7.46bn, N6.07bn da N6.77bn.

A 2020, kasafin abinci ya kwashe N483.78bn yayin da N6.98bn.

Amma a 2021, an samu ragowa inda abinci ya lashe N793.26m yayin da tafiye-tafiye suka cinye N5.228bn.

Wannan ragowar bata cigaba ba saboda an samu kari a kasafin kudin da aka mika wa majalisar tarayyar na 2022 inda abinci zai cinye N1.84m yayin da tafiye-tafiye za su cinye N5.29bn.

Kasafin kudin 2022: N31m kudin man Janareton Aso Rock, N22.07m na Gas din girki, N33m na littafai

A wani labari na daban, karin bayanai kasan daftarin kasafin kudin 2022 da Shugaba Buhari ya gabatar gaban majalisar dokokin tarayya na nuna cewa za'a kashe miliyoyin kudi don tabbatar da akwai wuta koda yaushe a fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Rahoto: Kudurorin gwamnatin Buhari da zasu jefa 'yan Najeriya cikin bakaken wahalhalu a 2022

Bayanai da Legit.ng ta tattaro cikin kasafin kudin ya nuna cewa ana bukatan N30.67 million domin sayan man feturin Janareton fadar shugaban kasa.

Hakazalika kasafin kudin ya bayyana cewa za'a yi amfani da N22.07 million wajen sayar iskar Gas na girki a 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng