Labari da dumi-dumi: ‘Dan Majalisar jihar Kaduna da ‘Yan bindiga su ka harba ya mutu
- A farkon makon nan aka ji miyagun ‘Yan bindiga suka bindige wani ‘Dan Majalisar jihar Kaduna
- Rahotanni sun tabbatar da cewa Rilwan Aminu Gadagau ya rasu bayan kwanaki biyu ya na jinya
- Hon. Rilwan Aminu Gadagau shi ne mai wakiltar mazabar Giwa a majalisar dokokin jihar Kaduna
Kaduna - Rahotanni marasa dadi su na zuwa mana cewa ‘yan bindiga sun hallaka daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar Kaduna a makon nan.
Honarabul Rilwan Aminu Gadagau mai wakiltar mazabar Giwa ta yamma a majalisar dokoki na jihar Kaduna, ya rasu a sakamakon harin ‘yan bindiga.
Daya daga cikin manyan ‘yan siyasar yankin Zaria, Malam Jamilu Albanin Samaru, ya tabbatar da wannnan labari dazu da safe a shafinsa na Facebook.
Jamilu Albani ya yi addu’a ga Ubangiji (SWT) ya karbi shahadar marigayin, ya yi masa rahama.
Allah Ya Karbi Shahadarka Hon Rilwan Aminu Gadagau. Allah Yasa Aljannah Makomarka.Allah Ya Tona Asirinsu Ya Hanasu Jin Dadin Duniya Da Lahira.
- Albani Samaru Zaria
Ya yi shahada a harin 'yan bindiga
Rilwan Gadagau ya na cikin wadanda ‘yan bindiga suka budawa wuta a ranar Litinin, 13 ga watan Disamba, 2021, wannan ne ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Majiyar mu ta shaida mana sai bayan kwana biyu da harbin ‘dan majalisar, sannan ya cika. Ya ziyarci Giwa a makon jiya ne domin ya ga 'yan mazabarsa.
A wani kaulin kuma, da yake bada sanarwar mutuwar Hon. Gadagau, shugaban karamar hukumar Giwa, yace ‘dan majalisar ya rasu ne tun kafin yau.
Hon. Rilwanu Aminu Gadagau aboki ne ga shugaban karamar hukumar Giwa, Abubakar Shehu Giwa, kamar yadda ya bayyanawa Duniya a dazu a shafinsa.
Za a birne Gadagau bayan sallar la'asar
'Yanuwan marigayin sun ce za ayi sallar jana'izarsa a masallacin Haruna Danja da ke daf da jami'ar Ahmadu Bello a unguwar Kongo bayan sallar la'asar.
Giwa ta na Arewacin Zaria, iyaka ne tsakanin Kaduna da Katsina. Garin na Giwa ya na cikin wuraren da ake fama da matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.
An yi ta'adi a hanyar Kaduna - Zaria
Idan za a tuna, ‘Yan bindiga sun yi barna a titin Kaduna zuwa garin Zaria a yammacin ranar Litinin, inda su ka sace mutane da-dama domin su karbi kudi.
Sojoji sun yi kokari wajen kubuto wasu daga cikin wadanda aka nemi ayi gaba da su. Amma kafin nan miyagun sun harbi mutane, har wani daga cikinsu ya mutu.
Asali: Legit.ng