Da Dumi-Dumi: Gwamnonin Arewa ta Gabas sun shiga ganawar sirri a Yobe

Da Dumi-Dumi: Gwamnonin Arewa ta Gabas sun shiga ganawar sirri a Yobe

  • Yayin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a Arewa, gwamnonin arewa ta gabas sun shiga ganawar sirri a Yobe
  • Shugaban kungiyar gwamnonin yankin, Gwamna Zulum, yace wannan taron shine karo na shida da zasu yi
  • Ya kuma yi kira ga jami'an tsaro su kara nunka kokarin da suke domin tsaftace yan ta'adda a yankin baki ɗaya

Yobe - Gwamnonin jihohi shida da suka haɗa yankin arewa maso gabas sun shiga ganawar sirri karo na shida a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Taron ya samu jagorancin shugaban gwamnonin kuma gwamnan Borno, Babagana Zulum kuma gwamna Mala Buni na Yobe ya karbi bakuncin shi.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da gwamna Zulum ya fitar a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Buhari, Gwamna Masari ya bayyana mutanen da suka kashe kwamishina a Katsina

Gwamnonin arewa ta gabas
Da Dumi-Dumi: Gwamnonin Arewa ta Gabas sun shiga ganawar sirri a Yobe Hoto: The Gobernor Of Borno State
Asali: Facebook

Gwamna Mala Buni na Yobe da gwamna Inuwa Yahaya na Gombe sun samu halartan taron yayin da gwamnonin jihohin Taraba, Adamawa da Bauchi suka tura wakilcin mataimakansu.

Da yake jawabin bude taron a gidan gwamnatin Yobe, Zulum ya yi bayani kan ayyukan kungiyarsu, da kuma ƙara jaddada kudurin ƙungiyar na tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Wane nasarori suka samu a yaƙi da ta'addani?

Shugaban gwamnonin yace cigaba da aka samu a yaki da ta'addanci kwanan nan wata alama ce ta kawo karshen matsalar tsaro a arewa maso gabas.

Ya kuma yi kira ga jami'an tsaron soji su ƙara zage dantse wajen share ta'addanci da yan ta'adda a yankin baki ɗaya.

Zulum yace:

"Ina kira da sojojin Najeriya su dumfari maɓoyar yan ta'adda waɗan ba su shirya aje makaman su ba, ya zama wajibi mu bi ta kansu.

Kara karanta wannan

Kawai ka alanta dokar ta baci a jihar Sokoto, Tambuwal ya bukaci Buhari

"Idan har muna son kawo karshen wannan rikicin sai mun tabbatar da an bi har maɓoyar yan ta'addan nan an aika su lahira."

Zulum ya ƙara da cewa har dai an kawo karshen Boko Haram sannan za'a fara ganin cigaba a dukkan jihohi shida.

Me gwamnonin suka maida hankali akai?

A jawabinsa na maraba, gwamna Mala Buni ya ƙara jaddada shirinsa na sadaukarwa ga kudirorin ƙungiya.

Buni ya yi tsokaci kan yanayin tsaro, da nasarorin da sojoji ke samu, da kuma bukatar masu ruwa da tsaki su cigaba haɗa karfi wajen yaƙi da yan ta'adda.

A wani labarin na daban kuma Abinda Shugaba Buhari ke yi kullum don kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya

A kullum shugaba Buhari sai ya yi maganar mutanen da ake kashewa tare da yi musu addu'a, inji fadar shugaban kasa.

Malam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, yace shugaba Buhari yana damuwa fiye da tunani kan halin rashin tsaro da ake ciki.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Jami'an DSS da yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a jihar Katsina

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: