Abuja: Rashin man fetur ya tsananta, jerin gwanon motoci ya dawo a gidajen mayuka
- Jerin layikan ababen hawa sun tsananta a cikin birnin Abuja wanda ake alakanta hakan da rashin man fetur a gidajen mayukan
- A yankunan Wuse da Jabi na Abuja, an ga wasu gidajen mayukan a rufe yayin da wasu ke bude amma babu man kwata-kwata
- An ga wasu 'yan bumburutu suna karakaina tare da kaiwa da kawowa da jarkokinsu na mai inda suka siyarwa da masu ababen hawa da ke bukata
Abuja - Jerin layin masu ababen hawa da ke neman mai a Abuja ya tsananta a ranar Litinin a babban birnin tarayya ya tsananta sakamakon matsalar karancin man fetur da aka fara.
Wannan ya na faruwa ne duk da tabbacin da NNPC ta bai wa 'yan Najeriya kan cewa za ta samar da isasshen man fetur a yayin lokutan shagulgulan bukukuwan karshen shekara.
Duk da har a halin yanzu ba a san takamaiman dalilin da ya kawo dogayen layukan ba, ana alakanta hakan da rashin man.
Wani wakilin Premium Times wanda ya ziyarci gidajen mayukan a ranar Litinin ya samu wasu daga cikinsu a rufe yayin da wasu kuwa babura suka cika su da masu adaidaita sahu tare da direbobi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An ga 'yan bumburutu suna ta tallar mai a jarkoki ga masu ababen hawa da ke da bukatar shi.
Gidajen mayuka masu yawa da ke yankunan Wuse da Jabi suna ta siyarwa da jama'a man a farashin N162 zuwa N165.
Gidan man Total da ke Wuse na kulle da tsakar ranar Litinin. Wani jami'insu ya sanar da Premium Times cewa, man fetur din ne ya kare karkaf.
Hakazalika, gidan man Azman Oil and Gas Nig Ltd da ke Wuse ya na bude amma wani jami'in ya sanar da cewa ba su da man, ya kare.
"Man ya kare da ranan nan amma muna tsammanin za mu samu wani da yammaci," yace.
Labari mai dadi: NNPC na kokarin ragargaza farashin gas, ta bayyana matakin da ta ke dauka
A wani labari na daban, Malam Mele Kyari, manajan daraktan matatar man fetur ta kasa (NNPC), ya alakanta tashin farashin gas din girki da yadda farashin danyen man fetur ya tashi a kasuwannin duniya.
Jaridar Guardian ta ruwaito cewa, Kyari ya sanar da hakan ne yayin kaddamar da ma'adanar kamfanin Emadeb Energy Services Limited mai daukar 120MT na LPG a Abuja.
Sai dai ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa, matatar na yin duk kokarin da ya dace wurin tabbatar da ta kara yawan LPG da ake samarwa domin ragargaza farashinsa, Guardian ta ruwaito hakan.
Asali: Legit.ng