Tsohon gwamnan Kano, Sanata Kwankwaso, ya yi magana kan rashin tsaro karkashin mulkin Buhari
- Yayin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a Najeriya, Kwankwaso yace bai taba tunanin zata girma haka ba a lokacin da yake ministan tsaro
- Tsohon gwamnan Kano, yace matsalar ba ta shugaban ƙasa bace kaɗai, domin sai an kammala komai ake faɗa masa
- Ya yi kira ga yan Najeriya a haɗa hannu wajen taimaka wa shugaban ƙasa, har a samu nasarar shawo kan lamarin
Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna damuwarsa bisa halin rashin tsaro da ake fama da shi karkashin mulkin Buhari.
Shugaban ɗarikar Kwankwasiyya a Najeriya ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa.
A cewar Kwankwaso, kyale matsalar da aka yi tun farko ba tare da ɗaukar tsauraran matakai ba, shine ya haifar da yawaitar lamarin har yake neman gagarar hukumomi.
Tsohon sanatan Kano ta tsakiya yace bai taɓa tsammanin matsalolin nan zasu girma haka ba, daga lokacin da ya bar ministan tsaro zuwa yanzu.
Kwankwaso yace:
"Wannan lamarin bana shugaban ƙasa bane shi kadai, mun san cewa sai an kammala komai sannan ake sanar da shugaban ƙasa. Amma batun ya sauya."
Meya jawo taɓarbarewan tsaro a Najeriya?
Kwankwaso ya bayyana cewa a hasashensa abubuwan da suka jefa Najeriya a cikin wannan yanayin sun kasu kashi-kashi.
"Na farko, shugaban ƙasa ya tafka kuskure, saboda a matsayinsa wajibi ya jawo kowa a tafi tare, da waɗanda suka tallafa masa da wandada ba su taimaka masa ba."
"Hakanan bai kamata mai rike da kujerar shugaban ƙasa, daga hawansa mulki ya nuna wane baya son sa, ko wane ba shi da amfani ba sam."
Menene mafita?
Jagoran tafiyar Kwankwasiyya yace mafita shine yan Najeriya su hada karfi da karfe wajen taimaka wa shugaban ƙasa a shawo kan kalubalen.
"A haɗa kai a nemo hanyoyin magance matsalar. Abun mamakin shine zaka ji an kashe mutane a wuri kaza amma gwamnati da jami'an tsaro ba zasu ɗauki mataki ba."
"Babban abun takaicin shine yan bindigan nan, kullum ƙara ƙarfi suke, suna samun kudi da kayan aiki, ka duba fa cewa ake suna karban haraji."
"A babbar kasa kamar Najeriya, wai ace wani ɗan ta'adda jahili ya samu ikon kwace wani wuri kuma an kyale shi, wai meke faruwa ne?"
A wani labarin kuma Kungiyar IZALA ta bada umarnin fara Alkunut a masallatan Ahlissunnah dake fadin Najeriya
Kungiyar Jama'atul Izalatil Bidi'a Wa'iƙamatis Sunnah (JIBWIS) wacce aka fi sani da Izala ta bada umarnin fara addu'oin Alkunut a masallatan Ahlissunnanh na faɗin Najeriya.
Shugaban kungiyar na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, yace idan muka tsarkake niyya Allah zai karbi rokon mu.
Asali: Legit.ng