Rahoto: Kudurorin gwamnatin Buhari da zasu jefa 'yan Najeriya cikin bakaken wahalhalu a 2022

Rahoto: Kudurorin gwamnatin Buhari da zasu jefa 'yan Najeriya cikin bakaken wahalhalu a 2022

  • Akwai matakai masu tsauri na tattalin arziki da gwamnatin Buhari ta tsara a shekarar 2022 wadanda dukkansu sun shafi 'yan kasar
  • Ana hasashen shekara mai zuwa zata yi wahala yayin da gwamnati ke shirin kwakule aljihun ‘yan Najeriya domin samun karin kudin shiga
  • Daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta zartas sun hada da tsauraran matakan haraji da kuma cire tallafin man fetur wanda ka iya dagula al'amura

Najeriya - ’Yan Najeriya na shirin shiga tsaka mai wuya a shekarar 2022, shekarar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke gab da barin Aso Rock.

Yayin da gwamnatin Buhari ke neman karin kudaden shiga domin biyan basussukan da ke kara yawa, za ta kwakule aljihun ‘yan Najeriya a shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kai farmaki sun kamo 'yan bindiga 30, sun ceto wani sarki da aka sace

Gwamnati ta ci gaba da kokawa da cewa tana da karancin albarkatun kasa don bi da yawan jama'a da ke kara yawa a kasar.

Ministar kudi ta Najeriya, Zainab Ahmad
Rahoto: Kudurin gwamnatin Buhari da zai jefa yan Najeriya cikin wahalhalu a 2022 | Luke MacGregor/Bloomberg
Asali: Getty Images

Za ta bi ta kowace hanya da ake da ita don samun karin kudin shiga don biyan basussuka, ta ci gaba da biyan ma’aikatan gwamnati har sai ta kai ga karshenta a 2023.

Duk wadannan bukatu na gwamnati dai daga bayan ‘yan Najeriya da ke fama da matsalar hauhawar farashin kayayyaki da suka ninka kudadensu, 33% cikin 100% na matasa marasa aikin yi, da tsadar rayuwa.

Buhari da majalisar ministocinsa na fafutukar tunkarar kalubalen tsaro da ba za a taba mantawa da su ba.

Kunji cewa, an kona mutane 23 yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa motar bus hari a Sokoto a makon jiya – fafutukar da ‘yan Najeriya ke fuskanta ita ce ta gwamnati na kara masa lamba don ganin ta kara fadada hanyoyin samun kudin shiga.

Kara karanta wannan

Yari Vs Matawalle: Kotu ta yanke hukunci kan rikicin jam'iyyar APC a Zamfara

Tallafin man fetur zai yi sallama da 'yan Najeriya

Matakan, kamar yadda gwamnatin tarayya ta sanar a sassa da dama, sun hada da dakatar da tallafin man fetur. Gwamnati dai ta nuna rashin jin dadinta game da shirinta na dakatar da tallafin man fetur.

N5,000 kudin zirga-zirga

Sai dai gwamnatin ta ce za ta rage wa 'yan Najeriya radadin cire tallafin ta hanyar biyan talakawan Najeriya alawus N5,000 duk wata na watanni shida na farkon 2022.

Kungiyoyin fararen hula da ma'aikata sun yi adawa da wannan matakin, inda suka ki amincewa da shi da cewa kudin ba zai magance komai ba.

TIN zai zama tilas ga masu asusun banki

Idan har sabon kudirin kasafin kudin da gwamnatin Buhari ta gabatar ya zama doka, zai kai ga gwamnatin Najeriya ta shiga wani yunkuri na karbar haraji a laluben da take na neman kudaden shiga don biyan basussukan da ke damunta.

Kara karanta wannan

Ba zata saɓu ba, Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan Kwamishina a jihar Katsina

Sabon kudirin dokar zai baiwa hukumar haraji a Najeriya damar kutsawa cikin asusun ajiyar ‘yan Najeriya domin ya zama tilas masu asusu su mallaki lambar tantance haraji ta TIN.

Zai zama wajibi ga mutanen da ke neman bude sabon asusun banki su nemo TIN daga Ma'aikatar Harajin Cikin Kasa ta Tarayya (FIRS).

Sabon kudirin dokar dai, idan har aka amince da shi, zai sa ‘yan Najeriya jigila tsakanin ofisoshin FIRS zuwa bankuna domin bude asusu, kamar dai yadda suka sha wahala wajen lika layukan waya da shaidar NIN ta kasa.

Kudin wuta zai yi mummunan tashi

Baya ga cire tallafin man fetur, kamfanonin da ke samar da wutar lantarki za su kara kudin wuta daga watan Janairun 2022 kamar yadda gwamnatin tarayya za ta kuma janye tallafinta bangaren wutar lantarki.

Kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito, gwamnati ta sanya mafi yawan kudaden tallafinta da take biya a fannin wuta wanda ya kai Naira biliyan 30 duk wata.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa muka haramta shan Shisha a jihar Kano, Yusuf Ibrahim Lajawa

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a wajen bude taron kungiyar IAEE na Najeriya karo na 14 kwanan nan a Abuja ya bayyana cewa, gwamnati na sa ran bangaren wutar lantarki zai samu kudaden shiga daga kasuwar wutar lantarki.

Dama can dai fannin wutar lantarki na daya daga cikin inda ‘yan Najeriya da ke son a samu ci gaba mai yawa.

Karin da aka yi a baya-bayan nan ya jawo 'yan sun Najeriya nuna fushi kuma yawancin masu amfani da wuta a kasar ba su da mitar gwada wutan lantarki.

Idan aka kara farashin wutar lantarki, hakan zai yi tasiri ga farashin kayayyaki da ayyuka domin masana'antu ma za su kara farashin kayayyakin da suke samarwa.

Wannan zai yi tasiri sosai kan harkokin sufuri, abinci da sauran ayyukan da suka dogara da wutar lantarki don gudanarwar yau da kullum.

Kakkausan kari a harajin VAT

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta fara wani yunkuri na neman karin harajin VAT wanda zai karu daga 5%5 zuwa 7.5% cikin 100% wanda kuma zai iya haifar da hauhawar farashin kayayyaki.

Kara karanta wannan

Buhari ya sha alawashin ladabtar da masu daukar aikin gwamnati ba bisa ka'ida ba

Rahotanni daga jaridar Vanguard sun ce wannan wani bangare ne na shirin kasafin kudi na shekarar 2022 wanda kuma ke bayyana a cikin dokar kasafi da bangaren zartarwa da gwamnati ya gabatar wa majalisar dokokin kasar.

Har ila yau, gwamnatin tarayya na sa ran samun Naira biliyan 29.3 a daga kudin za a caji 'yan Najeriya masu hada-hadar kudi a banki a wayoyinsu, wannan wata sabuwar hanya ce ta samun kudaden da za a aiwatar a shekarar 2022 a karkashin tsauraran matakan tara haraji.

Tuni dai harajin na VAT ya yi tasiri ga farashin kayayyaki kamar gas din girki da dai sauran su wadanda ya sa ‘yan Najeriya fadawa cikin kunci.

A 2022, ku shirya 'yan Najeriya, domin baku ga komai ba. Allah ya kawo sauki da dauki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.