5G zai taimaka wajen magance matsalar tsaro a Najeriya, Sheikh Pantami
- Ma'akatar sadarwa da tattalin arzikin zamani na shirin saka fasahar 5G a Najeriya bayan sahalewar gwamnatin tarayya
- Ministan sadarwa, Farfesa Pantami, ya bayyana hanyoyin da za'a bi wajen kawo karshen kalubalen tsaro da sadarwan 5G
- Pantami yace 5G zai taka muhimmiyar rawa a kokarin da hukumomin tsaro suke na kawo karshen yanayin da ƙasa ke ciki
Abuja - Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, yace 5G da ake shirin saka wa zai taimaka wajen shawo kan kalubalen tsaro a Najeriya.
Ministan ya yi wannan furuci ne ranar Litinin, a wurin taron gwanjon 3.5 GHz spectrum, wanda hukumar sadarwa ta kasa (NCC) ta shirya a Abuja.
Da yake jawabi a wurin taron kamar yadda The Cable ta rahoto, Pantami ya jaddada cewa sabis ɗin 5G ba shi da wata illa, kuma hukumar lafiya ta duniya (WHO) da kungiyar sadarwa ta ƙasa da ƙasa sun tabbatar da haka.
Ministan ya ƙara da cewa 5G zai taimaka sosai wajen kawo ƙarshen wasu daga cikin ƙalubalen tsaro a kasar nan, kasancewar fasahar tana samar da sabis mai ƙarfi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta ya fasahar 5G zata taimaka?
A jawabinsa yace:
"Muna tsammanin matukar 5G zata yi amfani a hukumomin tsaron mu, to zata taka muhimmiyar rawa wajen magance wasu daga cikin kalubalen da muke fama da su."
"Da farko 5G na da amfani fiye da 4G, 3G har da 2G, musamman wajen tantance bayanan sirri da kuma saboda sabis din 5G yana ƙunshe da fasaha."
"Dan haka wannan zai baiwa ma'aikatun tsaron mu wata dama na yin amfani da fasahar zamani kuma su saka sabbin fasahohin zamani wajen fuskantar kalubalen tsaro."
Ta ya wannan fasahar zatayi aiki a ɓangaren tsaro?
Pantami, wanda kwararre a ilimin sadarwa da kuma na'ura mai kwakwalwa, yace a zamanin da muke ciki idan zaka shawo kan matsalar tsaro kana bukatar sojojin roba, da tattara bayanai.
The Nation ta rahoto Pantami yace:
"A yanzu idan kana son magance kalubalen tsaro, kana bukatar sojojin roba, da tattara bayanan sirri. Duka waɗan nan fasahohin ba zasu yi wu ba sai da 5G saboda shine ke da karfin sadarwa."
"Da wannan fasahar da kuma karfin sadarwan dake tattare da shi, za'a iya amfani da abubuwan fasahar zamani wajen fuskantar tsaro."
A wani labarin na daban kuma Fadar Shugaban kasa ta bayyana irin matakan da shugaba Buhari ke ɗauka na kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya
A kullum shugaba Buhari sai ya yi maganar mutanen da ake kashewa tare da yi musu addu'a, inji fadar shugaban kasa.
Malam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, yace shugaba Buhari yana damuwa fiye da tunani kan halin rashin tsaro da ake ciki.
Asali: Legit.ng