Ana kashe mutane Shugaban kasa yana gantali – Aisha Yesufu ta sake ragargazar Buhari

Ana kashe mutane Shugaban kasa yana gantali – Aisha Yesufu ta sake ragargazar Buhari

  • Aisha Yesufu ta soki DSS a kan yunkurin takawa masu zanga-zanga burki a yankin Arewacin Najeriya
  • ‘Yar gwagwamayar tace abin da ya dace shi ne jami’an tsaron su kare rayuka, bah hana zanga-zanga ba
  • Yesufu tayi kaca-kaca da Shugaban kasa, tace ya tafi Legas a lokacin da ake kona mutanensa a jihar Sokoto

Aisha Yesufu ta fito ta koka a game da yadda jami’an tsaro suke muzgunawa matasan da suke kokarin fita zanga-zanga domin fadakar da gwamnati.

‘Yar gwagwarmayar tace babban abin da yake damun ta shi ne yadda jami’an tsaro suka hana mutane su fito su ce a gyara halin da ake ciki a kasar nan.

Legit.ng Hausa ta samu faifen wannan sako na Aisha Yesufu inda tace ana haramta zanga-zanga yayin da ‘yan bindiga suke yi wa al’umma ta’adi iri-iri.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: SSS ta gayyaci daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-zanga a Arewa

“Daga fitowa sun yi zanga-zanga, shikenan sai a rika fitowa ana kama su daya-bayan-daya, ana bin su ana kiransu, ana razana su.”
“DSS ba su da kunya, ba a kama wadanda ke kashe mutane, su na yi wa mata fyade ba, a’a, sai yaranmu da suka fito zanga-zanga.”

– Aisha Yesufu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan mata tace ya kamata a ba wadannan yara kariya, a samar da kasar da za su ji dadi. Ta ce don dole matasa suka fito suna yin wannan zanga-zangar.

Aisha Yesufu
Aisha Yesufu ta na zanga-zanga
Asali: UGC

“Akwai wanda yake son ya fito cikin rana? Akwai wanda ba ya son jin dadi ne, ya tsaya a cikin daula?”

Ba a so a fadawa Buhari gaskiya - Yesufu

Yesufu tace mai girma Muhammadu Buhari ba ya yin abin da ya kamata na kare jama'a, amma wasu sun hana a fada masa gaskiyar halin fatarar da ake ciki.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Fita Gari Sunyi Zanga-Zanga Kan Yawaitar Kashe-Kashe a Arewa

“Duk abin da ke faruwa a Arewacin Najeriya, shi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi shiru, ya yi kunnen-shegu, sai dai ya yi ta yawon gantali.”
“A wayi gari a kona mota kurmus, wai mu na da shugaban kasa tsohon soja, ya buga rigarsa ya tafi kaddamar da littafi a Legas, kuma a ce muyi shiru.”

– Aisha Yesufu

A guji zanga-zanga, a rungumi addu'o'i

Har ila yau, ta yi Allah-wadai da masu cewa ka da ayi komai sai addu’a a mulkin APC, tace bayan addu’a, Manzon Allah (SAW) ya kan fita yaki idan an taba shi.

A karshe Yesufu tace tun daga shugaban kasa, kowane ‘dan Najeriya cikakken ‘dan kasa ne, don haka babu wanda doka ta bada dama ga DSS su ci masa zarafi.

Mutane su rika yin Al-kunutu a Sallah - Sultan

Ganin cewa yawan zubar da jini ya yi yawa a Arewacin Najeriya, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III yace musulmai su dage da Al-kunut a masallatai.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ceto 'yan sanda 20 da 'yan ISWAP da Boko Haram suka yi garkuwa dasu a Yobe

Sarkin Musulmi ya bayyana wannan ne ta bakin kungiyar Jama'atu Nasril Islam wanda ta fitar da jawabi bayan an sace mutum fiye da 360 a watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng