Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un: Allah ya yi wa ɗan Sarki a Yobe rasuwa
- Allah ya yi wa Ibraim Tijjani Saleh, Hakimin Laruski kuma dan Mai Martaba Sarkin Gazargamu, Alhaji Tijjani Saleh Geidam rasuwa.
- Ya rasu ne a ranar Lahadi 12 ga watan Disambar 2021 a Maiduguri, Jihar Borno sakamakon hatsarin Keke Napep
- Mai Martaba Sarkin Gazargamu, Alhaji Tijjani Saleh ya tabbatar da rasuwar dan nasa, wanda ya rasu ya bar mata daya da yaya biyu
Jihar Yobe - Mazauna karamar hukumar Geidam na Jihar Yobe sun yi alhinin rasuwar Ibrahim Tijjani Saleh, Hakimin Laruski kuma dan Mai Martaba Sarkin Gazargamu, Alhaji Tijjani Saleh Geidam.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa sarkin ya tabbatarwa wa wakilinta rasuwar dan nasa cikin sakon kar ta kwana da ya aika.
Wata majiya daga iyalan sarkin ita ma ta tabbatar da rasuwar tana mai cewa marigayin ya rasu ne sakamakon hatsarin (Keke Napep) adaidaita sahu a ranar Lahadi a Maiduguri, Jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce:
"An garzaya da Hakimin Asibitin Koyarwa na Jami'ar Maiduguri nan take bayan afkuwar asibitin, amma daga bisani ya ce ga garin ku.
"Ya rasu yana da shekaru 30 da 'yan kai kuma ya bar matan aure daya da 'ya'ya biyu."
'Yan uwansa da abokan aiki sun bayyana mutuwar hakimin a matsayin babban rashi ga al'ummar Laruski, masarautar Gazargamu, Jihar Yobe da ma Najeriya baki daya.
Mai martaba sarkin Bade, Alhaji Abubakae Suleiman, ya mika sakon ta'aziyya ga mutanen masarautar Gazargamu, yana mai cewa za a rika tuna marigayin saboda halayensa na gaskiya, rikon amana da kaunar al'ummarsa da kokarin ganin cigaban masarautar.
Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa Na Najeriya, Janar Wushishi, Ya Rasu
A wani labarin, kun ji cewa Tsohon Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya a zamanin jamhuriya ta biyu, Janar Mohammed Inuwa Wushishi ya riga mu gidan gaskiya.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa majiyoyi daga 'yan uwansa sun ce yana wani asibiti ne a Landan yana da shekaru 81 a duniya.
Ya rasu ya bar mata daya, Kande Muhammadu Wushishi da 'ya'ya bakwai ciki har da tsohon Kwamishinan Saka Hannun Jari a Jihar Neja, Honarabul Kabiru Muhammadu Wushishi.
Asali: Legit.ng