Shugaba Buhari ba zai je Sokoto ba, amma ya tura IGP, NSA wakilci
- Shugaba Muhammadu Buhari ya tura tawaga ta musamman ka gaisuwar ta'aziyya Katsina da Sokoto
- Kusan dukkan manyan shugabannin tsaro a Najeriya na cikin wannan tawaga ta musamman
Shugaba Muhammad Buhari, a ranar Juma’a ya tura wakilai jihar Sokoto da Katsina bisa rashin rayukan da akayi kwanaki biyu da suka gabata sakamakon hare-haren yan bindiga.
Wannan ya biyo bayan ziyarar da Shugaban kasan ya kai jihar Legas ranar Alhamis.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma’a.
Ya yiwa jawabin taken ‘Shugaba Buhari ya tura Shugabannin tsaro da na leken asiri Sokoto da Katsina’.
A cewarsa,
“Shugaban kasa na jiran rahoton bincike da shawari kafin ya dau matakin magance lamarin.”
Wadanda Buhari ya tura sun hada da NSA, Major General Babagana Munguno; IG na yan sanda, Usman Alkali Baba; Dirakta Janar na DSS, Yusuf Magaji Bichi; Dirakta Janar na NIA, Ahmed Rufa’i Abubakar, da Shugaban leken asirin Soji, Major General Samuel Adebayo. I .
An yi jana'izar Kwamishanan Kimiyar jihar Katsina da aka kashe a gidansa
An gudanar Sallar Jana'izar Kwamishsnan Kimiya da Fasahan jihar Katsina, Dr Nasir Rabe, karkashin jagorancin Limamin Masallacin Katsina GRA, Dr Aminu Abdullahi Yammawa.
An bizne marigayin ne a makabartan Gidan Dawa bayan Sallar Jana'izar, rahoto DailyTrust.
Shugaban tawagar Gwamnatin tarayya yace Shugaban kasa ne ya tura shi jajantawa Gwamnatin jihar Katsina da iyalan mamacin.
Asali: Legit.ng