Kafin a birne shi, ‘Yan Sanda sun samu wani da hannu a kashe Kwamishinan Katsina

Kafin a birne shi, ‘Yan Sanda sun samu wani da hannu a kashe Kwamishinan Katsina

  • Jami’an ‘yan sanda na reshen jihar Katsina sun tabbatar da mutuwar Dr. Rabe Nasir a cikin gidansa
  • Kwamishinan ‘yan sanda ya bayyana cewa an kama wani da zargin hannu a kisan kwamishinan
  • Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya ziyarci gidan a lokacin da aka ga gawar Dr. Nasir

Katsina - Kafin a je ko ina, an ji jami’an ‘yan sanda na reshen jihar Katsina su na cewa sun kama mutum daya da ake zargi da laifin kisan kwamishina.

A ranar Alhamis, 9 ga watan Disamba, 2021, aka ji cewa an je har gida an kashe kwamishinan harkar kimiyya da fasaha na Katsina, Dr. Rabe Nasir.

A wani rahoto da jaridar Katsina Post ta fitar a ranar da abin ya faru, an ji cewa jami’an tsaro sun tabbatar da kama wani wanda ake zargi da laifin kisan.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamna Masari ya dira gidan kwamishinan da aka kashe, jami'ai sun cafke mutum daya

A sakamakon tashi tsayen da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Katsina, Sanusi Buba da darektan DSS na jihar suka yi, an kama wani da laifin kisan-kan.

Wanda ya yi wannan ta’asa, ya shiga rukunin gidaje na Fatima Shema da ke cikin birnin Katsina, inda ya aika da Dr. Nasir barzahu ba tare da wani dalili ba.

CP Sanusi Buba wanda ya ke shirin barin jihar Katsina bayan karin girma da aka yi masa a wurin aiki, yace tun a ranar Laraba aka kashe Kwamishinan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamishinan Katsina
kwamishinan kimiyya da fasaha na Katsina, Dr. Rabe Nasir Hoto: katsinapost.ng
Asali: UGC

Amma ba a tabbatar da mutuwar ba sai a ranar Alhamis 9 ga watan Disamba, 2021. Buba ya bada tabbacin cewa an kama wani da hannu a wannan kisan-kai.

Jaridar tace da aka zo daukar gawar Dr. Nasiru, an iske wayarsa da wayar wani mutumi a gefensa, wanda ake zaton shi ne ya yi wannan mummunan aiki.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An kashe kwamishina, Rabe Nasir, a gidansa da ke Katsina

Mutuwar kwamishina ta girgiza makwabtansa

Legit.ng Hausa ta nemi jin ta bakin makwabtan marigayin wadanda suka shaida mana cewa tun da yamma suka ji shigowar gwamna Aminu Masari cikin unguwar.

Wani mazaunin unguwar ya girgiza da jin mutuwar wannan Bawan Allah da suke sallah tare da shi idan ya na gida, yace sun yi mamakin ganin gwamna kwatsam.

An kashe kwamishinan kimiyya da fasaha

A baya kun ji cewa an kashe Rabe Nasiru dazu a gidansa. Rahoton yace an cakawa marigayin wuka sau uku a cikinsa, sannan aka rufe gawarsa a cikin kewaye.

A halin yanzu, an ajiye gawarsa a babbar asibitin tarayya na kula da marasa lafiya da ke garin Katsina. Ana sa ran a safiyar Jum’a za ayi wa Dr. Rabe Nasir jana’iza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng