Asiri ya tonu: Sojoji sun cafke Shugaban ‘Yan banga bisa zargin alaka da ‘Yan bindiga
- Rundunar Sojojin kasan Najeriya ta bayyana dalilin kama wani shugaban ‘yan banga a Kaduna
- Birgediya Janar Benard Onyeuko yace ana zargin Aminu Sani (Bolo) da laifin taimakawa ‘yan bindiga
- Da aka kama wani ‘dan bindiga a Igabi, ya hada Bolo da aiki, yace ya na cikin masu ba su hadin-kai
Kaduna – Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Rundunar sojojin kasan Najeriya ta bada sanarwa game da shugaban ‘yan bangan da ta kama a yankin Rigasa.
A wata sanarwa da ta fito daga bakin mukaddashin darektan yada labarai na sojoji, Birgediya Janar Benard Onyeuko, an tabbatar da kama Mal. Aminu Sani.
A ranar Alhamis, 9 ga watan Disamba, 2021, Janar Benard Onyeuko ya shaidawa manema labarai cewa sojoji sun yi ram da Aminu Sani wanda aka fi sani Bolo.
A cewar Janar Onyeuko, sojoji sun cafke Bolo ne a ranar Juma’ar da ta gabata a wani kauyen da ake kira Paka a karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna.
Jami’in yake cewa cafke wani gawurtaccen ‘dan bindiga da aka yi, ya jawo dakarun Operation Thunder Strike da na Operation Whirl Punch su ka kama Bolo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An jefi Bolo da babban laifi
Sojojin su na zargin shugaban na ‘yan bindigar sa-kai na JTF da samun alaka da ‘yan bindiga. Har yanzu ba a iya tabbatar da gaskiyar wannan zargi mai nauyi ba.
Wannan hatsabibin ‘dan bindiga da ya shiga hannun hukuma, ya shaidawa jami’an sojoji cewa shugaban ‘yan sa-kan ya na cikin masu taimaka masu a yankin.
Jami’an sojojin sun yi imani cewa Bolo wanda yake jagorantar CJTF, ya na taimakawa wajen sata da garkuwa da mutane da ake yi, a wasu lokutan har ana yi da shi.
Nasarar Operation Thunder Strike da na Operation Whirl Punch
An rahoto Janar Onyeuko ya na cewa dakarun Operation Thunder Strike da na Operation Whirl Punch sun kuma cafke wasu da ake zargi masu laifi ne a Igabi.
Baya ga haka, sojojin kasar sun yi nasarar datse wasu miyagu, tare da karbe wasu makaman su. Kawo yanzu ba a ji ta bakin Bolo, domin ya wanke kansa ba.
An kama shi da kan mutum
A jiyar Oyo, an ji jami’an tsaro na 'yan sanda sun cafke wani mutumi da ya shiga makabarta ya cire kan gawa a kabari, sannan ya saidawa baokinsa a kan N25, 000.
‘Yan Sanda sun kama wanda aka saidawa kan, daga baya aka cafke wanda ya ciro shi. Wannan mutumi da aka cafke, ya amsa laifin da ake zargin na sa da aikatawa.
Asali: Legit.ng