Kare ya fi ni daraja a idon mijina, Mata ta nemi alkali ya raba aurenta

Kare ya fi ni daraja a idon mijina, Mata ta nemi alkali ya raba aurenta

  • Wata Mrs Rashidat Ogunniyi ta bayyana gaban wata kotu a jihar Legas a ranar Alhamis inda ta shaida wa alkali cewa mijinta ya fi son karensa a kan ta
  • Matar mai shekaru 40 ta bukaci kotu ta raba aurensu mai shekaru 12 inda ta ce mijinta, Kazeem ya fi nuna muhimmanci akan walwalar karensa
  • A cewarta, tun da ta aure shi ba ta sake samun kwanciyar hankali ba, kuma ya mayar da ita kamar gangar-tashe tsabar dukan da yake mata

Legas - A ranar Alhamis wata mata mai suna Rashidat Ogunniyi ta bayyana gaban kotu inda ta yi wa alkali korafi akan yadda mijinta ya fi son karenta akan ta, Premium Times ta ruwaito.

‘Yar kasuwar mai shekaru 40 ta bukaci alkali ya warware igiyar aurensu mai shekaru 12 inda ta sanar da yadda hankalin mijinta ya fi karkata akan karensa.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari hazikar dalibata ce a darasin Physics, Malamar uwargidan shugaban kasa

Kare ya fi ni daraja a idon mijina, Mata ta nemi alkali ya raba aurenta
Matar aure ta fada wa kotu cewa mijin ta ya fi son kare a kanta. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Kamar yadda ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Kazeem ba miji ko kuma uba na gari bane, ba ya nuna min so balle kuma yaransa.
“Damuwarsa kadai akan karensa ta ke. Ya na nuna wa karensa so da kauna kwarai.”

Yana dukanta kamar jaka

Ta yi korafi akan yadda Kazeem ya ke cin zarafinta da dukanta kamar gangar tashe.

Ta shaida yadda wata rana ya taba dukanta a gaban jama’a tare da yaga mata sutturarta.

Har ila yau ta sanar da kotu ranar da ya tattara kayanta ya na yunkurin konawa, cikin gaggawa limaminsu ya kai mata dauki ya dakatar da shi daga yin aika-aikar.

A cewarta tun bayan aurensa ba ta kara samun kwanciyar hankali ba. Har sa yaransu yake yi su sato masa kudadenta don ya siya musu wayoyi.

Ta ce ta daina son Kazeem

Kara karanta wannan

Yar kasuwa ta damka wa kwastoma jakar kudin da ta mance a shagonta bayan wata uku, Yan Najeriya sun yi martani

Rashidat ta sanar da kotu cewa ta na bukatar a raba aurensu inda ta ce Kazeem ya sire mata, ta daina son shi.

A cewarta:

“Duk wani minti na rayuwata a firgice na ke. Ku cece ni daga hannun azzalumin mijina kuma a amsar min yara na, a taimaka min in rike su.”

Ya ki bayyana gaban kotu

NAN ta ruwaito yadda Kazeem ya ki bayyana a gaban kotun don sauraron zargin da ake yi masa.

NAN ta samu bayanai akan yadda kotu ta dade tana gayyatarsa amma ya ki amsa gayyatar.

Alkalin kotun, Mr Adeniyi Koledoye, ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Janairu don yanke hukunci.

A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu

A wani labarin daban, a ranar Litinin wata Firdausi Sulaiman mai shekaru 23 ta maka mijin ta, Haruna Haruna a gaban kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari a Kaduna tana bukatar a raba auren su da shi saboda yadda yake dukanta kamar gangar tashe sakamakon mungun cin abincin ta.

Kara karanta wannan

Ba Kayan Matan Jaruma Ne Ya Raba Aure Na da Laila Ba, Baƙin Halinta Ne – Biloniya, Ned Nwoko

Kamar yadda NewsWireNGR ta bayyana, a korafin da ta yi wa Kotu, Firdausi wacce take zama a Rigasa dake Kaduna ta ce har rufe kicin Haruna yake yi da dare.

Alkalin kotun, Nuhu Falalu, bayan sauraron bangarorin guda biyu, ya dage sauraron shari’ar har sai ranar 4 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164